Aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara, ne suka mutu da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke jihar Borno da ke a arewa maso gabashin Nijeriya .
Majiyoyi, ciki har da wani babba soja, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu da harin na baya bayan da safiyar ranar Talata, inda suka bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta tafiya Gamboru Ngala ne daga Rann lokacin da suka isa inda ‘yan ta’addan Boko Haram suka ɗana bam.
Baya ga mutum 26 da suka mutu, ƙarin mutum uku sun ji munanan raunuka.
Ƙaruwar hare-hare
“Mun tura wasu masu ba da agajin gaggawa inda lamarin ya auku domin kwashe mutane tare da tabbatar da tsaron sauran fararen-hula a wurin,” kamar yadda wata majiyar sojin da ba ta yarda a bayyana sunanta ba ta shaida wa Anadolu.
Ali Abass, wani ganau wanda ke tafiya a kan hanyar a lokacin da lamarin ya auku, ya ce sojojin da ‘yan sa-kai sun kai waɗanda suka jikkata wani asibiti. Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ‘yan’uwansa na cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Harin yana zuwa ne yayin da hare-hare ke ƙara ƙaruwa a yankin Tafkin Chadi, inda ‘yan ta’addan Boko Haram ke ƙara ƙaddamar da hare-haren bama-bamai da kwanton-ɓauna kan motocin fararen-hula da na sojoji.
An ba da rahoton hare-hare irin wannan a ranakun 21 ga watan Maris da 12 ga watan Afrilu. Kawo safiyar ranar Talata dai, jami’an tsaro a Borno ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba.