TURKIYYA
3 minti karatu
'Yadda Amurka ke bin tafarkin Netanyahu na da hatsari ga zaman lafiyar duniya' - Altun na Turkiyya
Sanarwar Daraktan Sadarwa na Turkiyya ya zo ne bayan da Amurka ta kaddamar da hare-hare a kan tashoshin nukiliya na Iran, ciki har da cibiyar Fordow, ta hanyar amfani da bama-bamai da kuma makamai masu linzami.
'Yadda Amurka ke bin tafarkin Netanyahu na da hatsari ga zaman lafiyar duniya' - Altun na Turkiyya
Harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran, tare haɗin gwiwar Isra'ila ba zai haifar da zaman lafiya ba / AA
23 Yuni 2025

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun, ya yi gargaɗin cewa hare-haren da Amurka ta kai a baya bayan nan kan cibiyoyin nukiliyar Iran, tare da haɗin gwiwar Isra'ila na zama wata babbar barazana da za ta ta'azzara tarzoma da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar yankin.

"Munanan hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran tare da haɗin gwiwar Isra’ila na nuna wani sabon mataki da zai haifar da ruɗani da tashe-tashen hankula, ba wai kawai ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya ba," kamar yadda Fahrettin Altun, Daraktan Sadarwa na Turkiyya ya bayyana a shafinsa na X a ranar Lahadi.

‘‘Kamar yadda tsarin shisshigin sojojin Amurka a Iraƙi da Afghanistan ya haifar da tsattsauran ra'ayi da ta'addanci a duniya, haka shi ma harin da Amurka ta kai kan Iran yake iya haifar da irin wannan sakamako."

Turkiyya ta sha yin kira da a sassauta rikici kana a yi zaman tattaunawa a matsayin hanyar samar da dawwamammen zaman lafiya a yankin. Sai dai sabbin abubuwan da suka faru, suna nuna yadda lamura suka yi muni tare da yiwuwar tasiri wajen mamaye Gabas ta Tsakiya.

Bayan hare-haren Amurka, Iran ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudanar da wani taron gaggawa domin yin Allah-wadai da harin wuce gona da irin na Amurka tare da hukunta duk wanda ya karya dokokin ƙasa da ƙasa.

‘‘Akwai alaka kai tsaye tsakanin shiga tsakani na sojojin Amurka da kuma sauye-sauyen da suka sake fasalin taswirar siyasar Turai ta hanyar haifar da kiyayya da kyamar addinin musulunci a yammacin duniya, tare da ingiza kyamar kasashen yamma da Amurkawa a yankin Gabas," in ji Altun.

"Idan Amurka ta ci gaba da bin tafarkin Netanyahu maimakon yin aiki don dakatar da manufofin yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila da kuma hana gwamnatin Netanyahu wadda ba ta ji ba ta kuma gani, zaman lafiya a duniya zai zama abu mai matuƙar wuya.’’

Rikicin dai, ya ɓarke ne a ranar 13 ga watan Yuni lokacin da Isra'ila ta kai hare-hare ta sama a wasu wuraren a faɗin Iran, ciki har da na soji da na cibiyoyin makaman nukiliya ƙasar, lamarin da ya sa Tehran ta kai hare-hare na mayar da martani.

Mahukuntan Isra'ila sun ce akalla mutane 25 ne suka mutu yayin da ɗaruruwa suka jikkata tun daga lokacin harin makami mai linzami na Iran.

A halin da ake ciki kuma, a Iran, mutane 430 ne suka mutu, yayin da sama da 3,500 suka jikkata a harin da Isra'ila ta kai, a cewar ma'aikatar lafiya ta Iran.

Muna kira ga al'ummomin duniya da su yi zanga-zanga kan abin da ya dace; a yi tsayin daka kan kokarin da wata kasa ke yi na tada hankali da zagon kasa ga tsarin kasa da kasa; da kuma ci gaba da jajircewa kan diflomasiyya wajen tunkarar batutuwan yanki da na duniya baki daya.” Inji Altun.

"A matsayinmu na al’ummar Turkiyya karkashin jagorancin shugaban kasar Recep Tayyip Erdoğan, za mu ci gaba da tabbatar da tsarin siyasa da zai kare zaman lafiya a yankinmu da ma duniya baki daya, da samar da zaman lafiya tsakanin al'ummomi, da samar da daidaito tsakanin Gabas da Yamma," a cewar Altun.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us