Turkiyya ta miƙa saƙon jaje da ta'aziyya bisa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a Jihar Neja da ke Nijeriya.
“Muna matuƙar alhini sakamakon rasa rayuka da lalacewar dukiya da mummunar ambaliyar ruwa ta haifar a yankin Mokwa na Jihar Neja a Nijeriya,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.
“Muna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma al’ummar Nijeriya baki ɗaya,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
Adadin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan a Mokwa ya kai fiye da mutum 150, a cewar sabuwar sanarwa daga hukumomi.
“Adadin waɗanda suka mutu yanzu ya kai 151,” in ji Ibrahim Hussaini, mai magana da yawun Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), bayan ruwan sama mai ƙarfi da ya sauka a ranar Laraba da daddare ya kuma ci gaba har zuwa Alhamis.
Ya bayyana cewa jimillar mutane “3,018 sun rasa matsugunansu sakamakon wannan bala’i. Kauyuka uku sun yi batan dabo.”
Ruwan sama mai ƙarfi ya haifar da mummunar lalacewa, inda ya shafe gidaje da kayayyakin more rayuwa, ciki har da hanyoyi da gadoji biyu.