SIYASA
7 minti karatu
Ana ci gaba da nisantar Netanyahu, Trump ma guje masa yake
A yayin da Trump ya tsallake Isra’ila a ziyararsa a Gabas ta Tsakiya, wannan waskiya na diflomasiyya na bayyana yadda duniya ke kara nisantar Netanyahu saboda abubuwan da yake yi a Gaza.
Ana ci gaba da nisantar Netanyahu, Trump ma guje masa yake
Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu and US President Donald Trump were close allies who are now reportedly no longer in direct contact, another sign of Netanyahu’s growing international isolation (Reuters). / Reuters
21 Mayu 2025

A lokacin da Shugaba Trump ya dawo zuwa Gabas ta Tsakiya a makon da ya gabata, ya kai manyan ziyarori zuwa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, amma ya tsallake Isra’ila.

Wannan tsallakewa ta janyo sanya idanu, musamman duba ga yadda aka san Trump da zama daya daga cikin manyan kawayen Isra’ila da kuma irin alakar da Firaminista Netanyahu a baya.

Masu kare Trump na cewa rashin zuwan nasa ba wai da gaske ba ne. Amma Washington Post sun rawaito cewa shugabannin biyu ba su da wata alaka ta kai tsaye, inda wani tsohon jami’in gwamnatin Amurka ya ce “Trump ba ya kallon darajar kulla alaka da shi.”

Mayar da saniyar ware ga Netanyahu na kara girmama sosai a tsakanin abokansa. Wanda ake kallon sa a matsayin babban mai fada a ji a yankinsu da kuma babban abokin Amurka, a yanzu Netanyahu ya zama shi kadai, wanda abububuwan da yake yi a Gaza ne ke janyo masa haka, da ma yadda yake bijirewa matsin lambar cikin gida da kasa da kasa.

A watanni ashirin da suka gabata, gwamnatin Isra’ila ta tsananta kai hare-hare Gaza - tun daga fara kutsa kai arewacin Gaza a watan Oktoban 2023, zuwa Khan Yunis a watan Disamba, sai Rafah a watan Mayun 2024, kafin dawo wa arewaci a watan Oktoba da sake afka wa Rafah da sauran yankuna a watan Maris din 2025.

Netanyahu ne mai bayar da umarni kai tsaye ga sojojinsu, wanda masu sanya idanu na kasa da kasa ke wa kallon hare-haren kisan kiyashi.

Duk da matsin lamba a gida da waje, nasarar da yake ganin ya samu na ci gaba da samun nuna rashin amincewa.

Kiraye-kiraye daga manyan kawaye, ciki har da Amurka, an yi biris da su baki daya. Hukuncin kotun kasa da kasa bai yi nasara ba.

Har ma bijirewa daga cikin rundunar sojin Isra’ila bai kai gaci ba; Netanyahu ba ya aiki da shawarwarinsu ko ma yana cin karo da su a bayyane.

An yi biris da masu adawa a cikin gida

A yayin da yakin ke ci gaba, an fara samun baraka a tsakanin sojojin Isra’ila. A watan Mayun 2024, shugaban sojojin Isra’ila a lokacin Herzi Halevi ya bayyana yanayin da ake ciki a Gaza da “ba mai karewa ba” yana sukar Netanyahu saboda rashin manufa mai kyau.

Wata bayan haka, kakakin rundunar Daniel Hagari ya fito karara yana tuhumar batun kakkabe kungiyar Hamas, yana mai bayyana ci gaba da samun rikici tsakanin Netanyahu da manyan shugabannin soji.

“Wannan aiki na rushe hamas, kakkabe Hamas baki daya - kamar watsa kasa a idanuwan jama’a ne,” in ji shi. Netanyahu ya yi watsi da wadannan gargadi tare da ci gaba da batunsa na neman “nasara baki daya”.

A lokacin tsagaita wuta ba watan Janairu, an samu goyon baya sosai na a kawo akrshen yakin, inda kashi 69 na ‘yan Isra’ila ke goyon bayan yarjejeniyar musayar fursunoni, ind akashi 21 suka nuna adawa da hakan.

Duk da haka, sai Netanyahu ya dowo yin ruwan bama-bamai a Gaza a ranar 19 ga Maris. A watan da ya biyo baya, wasu tsaffin sojojin isra’ila 1,000 sun sanya hannu kan takardar neman dawo war fursunonin yaki, ko da hakan na nufin dakatar da yakin.

Malaman jami’o’i da likitoci da tsaffin jakadu, dalibai da jagorori sun yi irin wannan kira. Amma a nan ma sai Netanyahu ya yi biris da su.

Wanda ya gaji Halevi, shugaban rundunar sojin Isra’ila Eyal Zamir, a baya bayan nan ya yi gargadi ga ministoci cewa kaddamar da sabbin hare-hare na iya jefa rayuwar fursunonin yaki cikin garari.

“Manufofin yakin guda biyu na karar da Hamas da kubutar da fursunoni na da matsala ga juna,” ya fada wa ministoci.

Netanyahu ya zama a waje guda. Ya bayyana “nasara” kan Hamas ba wai dawowar fursunonin yaki ba - shi ne babbar manufar yakin. A farkon watan Mayu, gwamnatinsa ta amince da fadada kai hare-hare, ciki har da shirin tirsasa wa fararen hula su yi gudun hijira daga arewacin Gaza.

Taurin kai da tirjiyar Netanyahu ta haura wajen Isra’ila. A watan Afrilun 2024, shugaban Amurka na lokacin Joe Biden ya gargadi Isra’ila kan afkawa Rafah baki daya, inda ya yi barazanar dakatar da ba su makamai idan ta shiga yankin.

Netanyahu ya yi biris ga gargadin inda ya kutsa kai, inda ya baje garin baki daya. Watanni shida baya, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa (ICC) ta fitar da hukunci a kamo shi saboda aikata laifukan yaki.

Martaninsa shi ne “Za mu ci gaba da yin duk abubuwan da suka zama wajibi mu yi.”

Kafin zuwan makon da zai kai ziyara Gabas ta Tsakiya, Shugaban Kasar Amurka ya bayyana fatan samun cigaba a tattaunawar da ake yi tsakanin Hamas da Isra’ila.

Amma sai Netanyahu ya kara danna kai: gwamnatinsa ta smaar da sabbin shirye-shiryen sake mamaye Gaza, tana rushe sauran gine-ginen da suka yi saura; tare da tirsasa wa Falasdiawan da ke da rai barin yankin zuwa '“yankin jin kai” guda daya tilo.

A yayin da bangaren Trump ke cewa tsallake Isra’ila a ziyarar ta Gabas ta Tsakiya ba wai da gan-gan ba ne, amma abinda ke a bayyana na fadin wani labarin na daban. Shugabannin biyu ba sa magana da juna kai tsaye.

Ministan Tsaron Trump ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Isra’ila, kuma jakadan Amurka ya bayyana karara cewa ba dole ba ne Amurka ta hada kai da Isra’ila don daukar mataki a yankin.

Har yanzu dai Netanyahu na nan a inda yake yana nuna tirjiya. “Isra’ila za ta kare kanta ita kadai idan hakan ta kama,” ya bayyana.

Ministan Tsaronsa, Isra’ila Katz, ya sake jaddada wannan matsayi, yana bayyana ko ba tare da Amurka ba za su tunkari barazanar yankin.

Sakamakon bijirewa

Tarihin taurin kai na Netanyahu na zuwa da sakamako. Yana tsawaita yakin sama da irin yake-yake gajeru da Isra’ila ta saba yi.

Sama da kasashen duniya goma sun raga girman alakarsu da Isra’ila, inda wasu kuma da suka hada da Spaniya, Ireland, Slovenia, da Norway - a hukumance sun amince da ‘yantacciyar kasar Falasdinu.

Faransa ta nuna alamun za ta bi sahu.Matsayin Isra’ila a duniya ya lalace, har ma a wajen manyan kawaye irin su Amurka.

Sannan ga sakamakon shari’a, an kai karar kisna kiyashi a Kotun Hukunta Manyan Laifuka da karar aikata muggan laifuka a Kotun Kasa da Kasa.

A cikin gida, matsin tattalin arziki na daduwa. Darajar bayar da bashi ta ragu, an dakatar da gine-gine, sannan yawon bude ido ya ragu.

Gudun hijira ya dadu da kashi 285 a 2024, inda kusan rabin ‘yan Isra’ila ke duba yiwuwar barin kasar saboda rashin tsaro da ke naman mayar da kasar daga daga wurare mafi rashin tsaro da kuma hatsari ga ‘yan kasarta.

A yayin da matsin lamba ke karuwa, tambayar ba ita ce ko dabarun Netanyahu za su yi nasara ba, Ita ta ko ‘nasara baki daya’ ta yi illa ga kasar da yake cewa yana karewa.

Dan-jaridar Isra’ila Ben Caspit kwanakin baya ya yi tambayar “Mene matsalar nasara saki ba kaidi?” sai ya amsa da kansa: “Babu matsala, kawai sai dai cewa babu wannan abu kwata-kwata. Babi shi gaba daya. Mafarki ne. Tunanin abinda babu shi ne.”

Tsohon shugaban Shin Bet, Ami Ayalon ma ya bayyana irin haka a watan Yuli, yana mai nacewa kan fadin babu mafita ta hanyar sojoji su yaki Hamas.

Hanya daya mafi nasara ita ce a bayar da shawara mai kyau da Isra’ila da Falasdin.

Amma Netanyahu, da yake da mugunyar siyasa da taurin kai, ba ya neman shawarwari masu kyau.

Dabarunsa sun jefa Isra’ila cikin rikicin da ya ki zuwa karshe, wanda ke kawo asara da yawa. Kuma nannan balahira na iya sauya ne watakila idan ‘yan Isra’ila suka zabi sabon shugabanci.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us