NIJERIYA
2 minti karatu
Netherlands ta miƙa wa Nijeriya kayayyakin tarihi 119 da aka sace daga Benin
An mayar da kayayyakin tarihin ne bisa buƙatar Hukumar Kula da Gidajen Tarihi ta Nijeriya.
Netherlands ta miƙa wa Nijeriya kayayyakin tarihi 119 da aka sace daga Benin
Sojojin Birtaniya sun yi wa Masarautar Benin fashi a shekarar 1897. / TRT Afrika Hausa
20 Yuni 2025

Netherland ta mayar da kayayyakin tarihi har guda 119 da aka sace daga Nijeriya, wadanda suka hada da gumakan mutane da dabbobi da alluna da kuma kayan sarauta da na ƙararrawa a ranar Alhamis.

Kayayyakin sassakar na tarihi da aka fi sani da Benin Bronzes, wadanda galibinsu aka ajiye su a wani gidan tarihi a birnin Leiden, sojojin Birtaniya ne suka sace su a ƙarshen ƙarni na 19.

Mayar da kayayyakin daga Netherlands na daga wani ɓangare na faɗaɗa yunkurin duniya. Gidajen tarihi a dukkan faɗin Turai da Arewacin Amurka suna ƙara fuskantar matsi da ƙalubalen kan kayan tarihin da aka sace a lokacin mulkin mallaka.

A shekarar 2022 kadai, Nijeriya ta nemi a mayar da daruruwan kayayyakin tarihinta a duniya baki daya, inda aka mayar da 72 daga gidan adana kayan tarihi na Landan, sai kuma 31 daga gidan tarihi na Rhode Island.

“Taimako daga Ubangiji”

A yayin bikin miƙa kayayyakin a jihar Edo, Sarki kuma mai kula da al’adun Benin, Oba Ewuare II, ya bayyana mayar da kayayyakin a matsayin “Taimako daga Ubangiji.”

"Mayar da kayayyakin tarihin wata shaida ce ta karfin addu'a da azama," in ji sarkin.

Kazalika gwamnatin Holland ta ce ta kuduri aniyar mayar da kayayyakin tarihi da ba na kasarta ba, in ji Marieke Van Bommel, daraktar gidan adana kayan tarihi na Wereld.

Olugbile Holloway, daraktan hukumar kula da gidajen tarihi ta Nijeriya, ya ce mayar da kayayyakin tarihi 119 ƙasar y zama kayayyaki mafi yawa da aka mayar da su kawo yanzu, kuma hukumar na aiki tukuru don ƙwato wasu kayayyakin da aka sace a lokacin mulkin mallaka.

An sace Bronzes na Benin ne a shekara ta 1897 lokacin da sojojin Birtaniya ƙarƙashin jagorancin Sir Henry Rawson suka kai wa Masarautar Benin hari tare da tilasta wa Ovonramwen Nogbaisi, sarki na lokacin, gudun hijira na watanni shida. Benin na daga cikin yankin kudancin Nijeriya a wannan zamani.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us