NIJERIYA
2 minti karatu
Matatar Dangote za ta fara dakon fetur da dizal kyauta a faɗin Nijeriya
Domin tabbatar da fara wannan shirin cikin kwanciyar hankali, sanarwar ta ce matatar ta sayi tankokin dakon mai masu amfani da iskar gas (CNG) guda 4000.
Matatar Dangote za ta fara dakon fetur da dizal kyauta a faɗin Nijeriya
Matatar man Dangoteta ce wannan shirin nata zai sauya harkar saya da sayar da mai a Nijeriya / Dangote
16 Yuni 2025

Matatar man Dangote ta yi shelar cewa za ta fara dakon man fetur da dizal zuwa gidajen mai da sauran masu buƙatar man a faɗin ƙasar.

Wata sanarwa da kamfanin Dangote ya fitar ranar Lahadi ta ce shirin wanda zai sauya harkar saye da sayarwar mai a ƙasar zai fara aiki ne daga ranar 15 ga watan Agustan wannan shekarar.

“Daga ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2025, matatar za ta fara dakon man fetur da dizal ga ‘yan kasuwa da dillalan fetur da masana’antu da kamfanonin sadarwa da masu jiragen sama da kuma sauran masu amfani da mai da yawa a faɗin ƙasar a kyauta domin inganta yadda ake rarraba [mai],” in ji sanarwar.

Domin tabbatar da fara wannan shirin cikin kwanciyar hankali, sanarwar ta ce matatar ta sayi tankokin dakon mai masu amfani da iskar gas (CNG) guda 4000.

“Wannan matakin zai ci gaba da gudana zuwa lokaci mai tsawo. Matatar tana kuma zuba jari wajen samar da tashoshin iskar gas na mota (CNG) tare da tankokin dakon iskar gas na CNG 100 a faɗin ƙasar domin tabbatar da rarraba [mai] ba tare da wata matsala ba,” a cewar sanarwar.

Matatar ta ce shirin ɗaya ne daga cikin matakan jajircewar matatar wajen kawar da kuɗin dakon mai da inganta samar da makamashi da kuma taimaka wa ci-gaban tattalin arzikin ƙasar.

 Kazalika sanarwar ta ce matatar za ta ba da damar sayen lita 500,000 a bashi ga duk wanda ya sayi lita 500,000 bisa sharaɗin samun bankin da zai tsaya masa.

Duk da cewa matatar man Dangote fara aiki, wasu dillalan mai dai sun ci gaba  da shigo da tataccen mai cikin ƙasar daga ƙetare.

Wasu na ganin wannan matakin da matatar ta Dangote ta ɗauka zai iya tasiri kan ayyukan dillalai masu shigo da tataccen mai daga ƙetare.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us