Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi kakkausan suka ga hare-haren da Isra’ila ta kai Iran, inda ta kira su da karya dokar ƙasa da ƙasa da tsokanar faɗa da yin barazana ga zaman lafiyar yankin da ma duniya baki ɗaya.
“Muna sukar hare-haren da Isra’ila ta kai wa Iran da babbar murya, waɗanda suka saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa,” in ji ma’aikatar a sanarwar.
“Wannan tsokanar faɗa ce da ke bayyana manufofin Isra’ila na dagula al’amura a yankin.”
Ankara ta ce lokacin da aka kai harin na bayyana yadda gwamnatin Isra'ila ba ta son aiki da diflomasiyya.
“Lokacin da aka kai hare-haren na nuni da cewa gwamnatin Netanyahu ba ta da niyyar warware wani rikici ta hanyar diflomasiyya kuma tana son jefa zaman lafiyar yankin da na duniya baki ɗaya cikin hatsari saboda buƙatar kanta,” in ji sanarwar.
Ma’aikatar ta yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da hare-haren soji da take yi nan-take.
“Dole ne Isra’ila ta dakatar da ayyukanta na fusatawa, waɗanda na iya janyo ƙarin rikici,” in ji sanarwar, tana mai jaddada matsayin Turkiyya na nuna adawa ga ƙarin zubar da jini a yankin.
“Muna jaddada cewa ba ma son ganin ƙarin zubar da jini da rusau a Gabas ta Tsakiya,” ma’aikatar ta ƙara bayyanawa, tana mai kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki mataki.
“Muna kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matakan gaggawa don hana yaɗuwar yakin.“
Sabawa doka da tsokana: Mataimakin Shugaban Ƙasa Yilmaz
Mataimakin Shugaban Ƙasar Turkiyya Cevdet Yilmaz ma ya soki hare-haren na Isra’ila, yana bayyana su da “haramtattu kuma na tsokana.”
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Yilmaz ya ce “Da kai wa Iran hari, Isra’ila ta sake aikata wata takalar faɗa haramtacciya a tarihinta. Muna suka da babbar murya ga gwamnatin Netanyahu wadda ba ta da wani dalili na rikita yankin. Muna mika saƙon ta’aziyya ga Iran saboda asarar rayukan da aka samu.”
“A lokacin da ƙasashen duniya ke matsa lamba ga Isra’ila kan kisan kiyashin da take yi a Gaza da tattaunawar Nukiliyar Iran da ake ci gaba da yi, wannan hari na bayyana halayyar dabbobi da biris da darajar ɗan’adam da diflomasiyya,” ya ƙara fada.
Yilmaz ya yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki tsayayyen mataki, “Dukkan cibiyoyin ƙasa da ƙasa da ƙasashen duniya ya zama dole su ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan ayyukan Isra’ila da ke barazana ga ɗan’adam, dokokin ƙasa da ƙasa da zaman lafiyar yankin.”
Altun Turkiyya za ta ci gaba da aiki don zaman lafiya: Altun
Daraktan Sadarwar na Turkiyya, Fahrettin Altun, ya yi suka da babbar murya ga harin na Isra’ila a wata sanarwa da ya fitar ta shafin X, yana mika ta’aziyya ga jama’ar Iran da ƙasar.
“Muna suka da babbar murya ga harin da Isra’ila ta kaiwa Iran kuma muna miƙa ta’aziyya ga jama’ar Iran da gwamnatin ƙasar,” in ji Altun a ranar Juma’a.
Ya yi gargaɗin cewa harin na sake bayyana barazanar da gwamnatin Netanyahu ke yi wa zaman lafiyar yankin da duniya baki ɗaya.
“Wannan hari ya sake bayyana wa ƙasashen duniya irin hatsarin da kisan kiyashin da gwamnatin Netanyahu ke yi ga yankin da ma duniya baki ɗaya.”
Altun ya soki kasashen duniya saboda nuna halin ko-in-kula tun bayan fara kisan kiyashin Isra’ila a Gaza, yana mai cewa: “Shirun da ƙasashen duniya suka yi ne ya baiwa rikicin damar yaɗuwa, yana kona yankin baki ɗaya da jefa duniya cikin rikici.”
Ya ƙara da cewa gargaɗin da Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi game da halin fusata da Isra’ila ke nunawa ya bayyana.
Altun ya jaddada cewa dole ne a yanzu a auna hare-haren Isra’ila ta mahanga da yawa - daga makamashi da tattalin arzikin duniya zuwa ga dokokin kasa da kasa da diflomasiyya.
“Dole ne kasashen duniya su dauki mataki don kare zaman lafiyar duniya da yankin, da kuma daukar matakin dakatar da hare-haren Isra’ila a yankin.”
“Turkiyya za ta ci gaba da aiki don zaman lafiya a yankin da ma duniya, da kalubalantar haramtattun ayyukan Isra’ila, da goyon bayan duk wani kokarin da ke son kawo hakan.”
‘Wautar Isra’ila barazana ne ga duniya baki daya’
A gefe guda, Jam’iyyar AKP mai mulki a Turkiyya ta ce harin na ba zata da Isra’la ta kai wa Iran “ba shi da halasci ko madogara.”
“Wannan mummunan hali ne,” in ji kakakin jam’iyyar Omer Celik, a sakon d aya fitar ta shafin X a ranar Juma’a.
Tare da wannan harin, Isra’ila ta kara “kai hare-hare don lalata zaman lafiyar yankin,” in shi, yana sukar “haramcin” da babbar murya.
Dukkan duniya na bukatar aiki da gargadin Shugaban Kasar Turkiyya game da sakamakon da ke biyo bayan kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ke yi karkashin Firaminista Netanyahu.
An kashe masanan nukiliya
A yayin da duniya ke matsa lamba game da Isra’ila kan kisan kiyashin da take yi a gaza, a yanzu ta sake kai wani harin don kawar da hankulan duniya daga kan Gaza, in ji Celik.
Harin da Isra’ila ta kai a yayin da Amurka da Iran ke tattaunawa kna Nukiliya “Isra’ila a koyaushe na adawa da kokarin diflomasiyya,” in ji shi.
Isra’ila ta kai harin soji kan Iran a ranar Juma’am inda jiragen sama 200 suka hari cibiyarta ta nukiliya da makamanta masu linzami da ke cin dogon zango. An kashe manyan masanan kimiyyar Iran a harin.