Babbar manufa na samar da manyan mutane, kamar yadda ake fada, kuma Sarki Fatih Sultan Mehmed ya zama babban mutum da aka haifa.
A wannan rana, shekaru 572 da suka gabata, Sarki Sultan Mehmed II ya yaki Daular Byzantine inda ya kwace birnin Istanbul tare da kawo karshen Daular Gabashin Rum.
Mehmed da a lokacin yake da shekaru 21 kawai, ya dora Daular Usmaniyya kan samun babban sauyi da cigaba.
Ga takaitaccen tarihin nasarar da Sarki Sultan Mehmed II ya yi.
An haifi Sultan Mehmed mayaki a ranar 30 ga Maris din 1432 a Edirne, wanda nan ne babban birnin Daular Usmaniyya a wancan lokacin. Mahaifinsa Sultan Murad II ne Sarkin Daular Usmaniyya na lokacin.
Mehmed ya zauna a Edirne har zuwa shekara biyu, An tura shi Amasya a 1434, inda yayansa Ahmad, mai shekaru 14 yake gwamnan Sanjak tare da dan uwansa Aleddin Ali.
Domin ilimantar da Mehmed, mahaifinsa ya samar da malamai daban-daban. Amma Mehmed, wanda yake da kwarewa a yaki kamar yadda yake da kaifin kwakwalwa, babu saiki wajen ilmantar da shi.
Malaman Musulunci da na Boko ne suka karantar da Mehmed. Duk da an fi sani da yabon Sarkin na Daular Usmaniyya da jarumtarsa ta yaki, gudunmawarsa ga fannin falsafa, kimiyya d fasaha ma na da yawa da kima.
An ce Mehmed na magana da yarukan Fashanci, Larabci, tsohon Yaren Girka da Italiyanci - wanda d ayawa ke kallon alamu ne na bayyana burinsa na kafa Daular da ta fadadu har zuwa kasashen Yamma da Gabas.
Malaman tarihi na Turkiyya na cewa dakin karatunsa na dauke da litattafan da suka shafi lissafi, addini, injiniyanci, ilimin taurari, ilimin snain zamantakewa da falsafa.
An san shi da zama marubucin waka, mayakin kuma na da sha’awar kimiyya, inda har ya sanya mai zane Bellini ya zana hotonsa.
Watakila Sarkin na Daular Usmaniyya ya tasirantu da rayuwar Alexander mai Girma a kokarinsa na kafa dauka, saboda ya karanta yadda ya yi kokarin jagorantar sojoji.
Homer’s Iliad na daya daga litattafan da ke dakin karatunsa, kuma sannan akwai tsohuwar taswirar duniya ta Ptolemy a kayayyakinsa.
An haishe don ya yi mulk
Mehmed dogo ne, mai kumatu, da lankwasasshen hanci. mai kwanji kuma kakkarfa da ya mayar da hankali ga karance-karance.
Ya karanta nlitattafan falsafa da aka fassara zuwa yaren Fasha da Larabci.
A batutuwan kimiyya, ya bayar da kariya ga malamai, ba ruwan sa da addini ko bangaren da kake bi, sannan ya buga litattafansu.
A yayin kokarin bayyana kansa a bainar Usmaniyyawa, tare da kuma kokarin cim-ma burinsa na kafa tarihi, ya dasa idanuwansa kan ya za a yi ya kwace birnin Costantinople - wanda a lokacin yake babban birnin Daular Usmaniyya. Sai ya yi shiri na musamman don yakin da ke tafe.
Duk da cewa birnin ya fuskanci mamaya a lokuta daban-daban a baya, babu wanda ya samu nasarar kwace shi, kuma Mehmed II ya sani sarai cewa yin abinda ya gagara na bukatar dabaru na musamman da hangen nesa.
Sarkin ya tara runduna mai girma (sama da dakaru 200,000), amma wasu masu tarihi na cewa adadin bai kai haka ba, bai ma fi rabin hakan ba, wadand asuka bayyana a gaban ganuwar birnin da karfin gwiwa.
Ya zagaye birnin ta ruwa da ta kasa, sannan ya kai korar da ba a zata ba: jibge jiragen ruwan yaki a tashar jiragen ruwa ta Galata - da ke gabar mashigar tekun Istanbul a bangaren Turai na birnin.
Jami’an sojin sun ci gaba da kai komo da gangami na tsawon kwanaki 50, inda ake ta harba manyan bam don fasa katangar shiga birnin ta yadda sojoji za su iya kutsa kai.
A ranar 29 ga Mayu, birnin ya fadi baki daya, inda Mehmed II ya samu matsayin ‘Fatih’ wanda ya yi nasarar yaki.
Matashin Jarumi
Jarumi kuma Mayaki Mehmet na da shekaru 21 kawai a lokacin da ya ruguza Daular Byzantine tare da mayar da ita tarihi, inda ya mayar da Daular Usmaniyya mai jagoranci a yankunan duniya da dama na nahiyoyi uku.
An fi sanin nasarar yakar birnin da nasarar Mehmed II, amma a shekarun da suka biyo baya ya tabbatar da Daular Usmaniyya ta kwace iko da Serbia, Trebizond (Trabzon a yau) a arewacin Turkiyya ta yau da ma Bosnia, Albania da wasu yankunan tsakiyar Anatolia da ke cikin Turkiyya.
Ya kasance a kan mulki har zuwa 1481 inda ya halarci yake-yake har 25, ya mayar da Istanbun babban birnin daular, wadda iyakokinta suka fadada tun daga Tafkin Danube zuwa Tafkin Kizilirmak
Sarkin ya yi nasarar yakar iyakoki da dama, ya kara yawan kasar da Daular Usmaniyya ke jagoranci zuwa sukwaya kilomita miliyan 2.2.
A shekarar 1480 ne aka rera wakar nasarar Mehmed II a lokacin da ya yi nasara a Otranto, Italiya, inda yake shirin matsawa zuwa Rum. Amma ya rasu a ranr 3 ga Mayun 1481.
Masana tarihi a Turkiyya na muhawarar ko yana da niyyar shiga Rum, wanda hakan ya kwace iko da Otranto.
Da a ce a shi da niyyar hakan to da ya mayar da hankali ga karbe bangaren gabas.
Mayakin, wanda ya yi nasarar yake-yake da dama, tare da kula da kwace Istanbul da garuruwa da yawa a shekaru 49 na rayuwarsa, ya bar tabon da ba zai gogu a tarihi ba, kuma manufofinsa na nan har yanzu ana amfana da su.