A ranar Laraba ne manyan jiga-jigan ‘yan siyasa suka hallara a Abuja inda suka zaɓi jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su yi amfani da ita wajen tunkarar gwamnatin Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
‘Yan siyasar sun haɗa da tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, David Mark da aka naɗa shugaban ADC na riƙo da tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da aka naɗa sakataren riƙo na jam’iyyar.
Har ila yau a cikin jigajigan ‘yan siyasar akwai tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon ministan Abuja, Nasir El-Rufai da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da tsohon babban lauyan Nijeriya, Abubakar Malami da kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma tsohon ɗan takaran shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar Labour (LP) a zaɓen 2023.
Tun bayan da jiga-jigan ‘yan adawan suka bayyana jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su yi amfani da ita wajen tunkarar gwamnatin APC a zaɓen 2027 ɗin ne dai magana kan haɗakar ta karaɗe Nijeriya inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa.
Wa’adin sa’o’i 48
Jam’iyyar Labour Party (LP) na cikin waɗanda suka fara tsokaci game da haɗakar inda ta bai wa ɗan takaran shugaban ƙasarta a shekarar 2023, Peter Obi, wa’adin sa’o’i 48 ya yi murabus bayan ya shiga haɗakar ‘yan adawan ta ADC.
A watan sanarwar da ya fitar a Abuja, sakataren jam’iyyar LP, Obiora Ifoh ya bayyana haɗakar a matsayin gungun masu kama karya inda ya zargi Peter Obi da yi wa jam’iyyu biyu mubaya’a.
“Mun san da wasu tarurruka na cikin dare tsakanin Peter Obi da wasu ‘yan jam’iyyarmu, yana zawarcinsu [domin] su bi shi sabuwar jam’iyyarsa. Muna sane kuma cewa wasu daga cikinsu sun ƙi su sauya sheƙa tare da shi,” a cewar Ifoh.
Ya ƙara da cewa LP ba ta cikin haɗakar kuma ba za ta lamunci kasancewar mambobi masu biyayya ga jam’iyyu biyu a cikinta ba.
“Labour Party ta sha nanatawa cewa ita ba ta cikin wata haɗaka, kuma saboda haka duk wani mambanmu da ke cikin haɗakar mun ba shi wa’adin sa’o’i 48 ya fice daga jam’iyyar,” in ji shi.
Sai dai kuma tsohon ɗan takaran shugaban ƙasar jam’iyyar bai mayar da martani ba tukuna ga wa’adin da LP ta ba shi na ficewa daga cikinta.
Har wa yau wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP na cewa ya kamata jam’iyyar ta hukunta waɗanda aka gani a wajen taron ayyana ADC a matsayin jam’iyyar haɗakar ‘yan hamayyar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, wanda shi ma ɗan jam’iyyar PDP ne bai mayar da martani ba game da wannan maganar ta hukunta ‘yan jam’iyyar da suka halarci taron haɗakar.
‘Muhimmancinsu bai kai yadda ake kambawa ba’
Kazalika mai ba wa shugaban Nijeriya shawara na musamman kan watsa labarai, Bayo Onanuga ya ce yawancin waɗanda ake cewa sun fice daga APC zuwa ADC a haɗakar sun daɗe da ficewa daga jam’iyya mai mulkin.
A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Onanuga ya ce muhimmancinsu a jam’iyyar APC ɗin bai kai yadda ake kambawa ba.
“Rotimi Amaechi ya bar APC a shekarar 2022 bayan ya sha kaye a zaɓen fidda gwani a hannun Shugaba Tinubu,” in ji Onanuga.
“Abubakar Malami, tsohon babban lauyan Nijeriya, bai taɓa ɓoye rashin jituwarsa da APC ba tun da Tinubu ya karɓi ragamar mulki kuma ya kasa cim ma burinsa na zama gwamna a jihar Kebbi,” a cewar saƙon.
Onanuga ya ce Rauf Aregbesola kuma ya yaƙi jam’iyyar a zaɓen jihar Osun na baya kana aka kore shi daga jam’iyyar a matsayin wanda bai dace ya kasance ɗan jam’iiyyar ba.
“Hadi Sirika, wanda a yanzu yake tare ADC, yana fuskantar shari’a kan rarraba kwagila da sauran zarge-zarge, in ji Onanuga.
‘Ban fice daga APC ba’
Minstan Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, Nyesom Wike ma ya bi sahun waɗanda suka soki haɗakar inda ya ce mambobin haɗakar ciki har da Rotimi Amaechi da Abubakar Malami da kuma Hadi Sirika sun samu damar gyara Nijeriya, amma ba su yi abin a zo a gani ba.
Sai da kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya ce shi ya ji mamakin cewa an ce shi yana cikin ‘yan haɗakar saboda shi yana tare da APC idan har tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana cikinta.
“Ina cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC, ni na ba ta sunanta. Ba ni da niyyar barinta. Zan ci gaba da kasancewa inda Shugaba Buhari yake. Idan ya zama dole ka tsane shi, to ka tsane ni nima,” kamar yadda ya bayyana a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.