NIJERIYA
4 minti karatu
Jama'ar Mokwa na ci gaba da fatan samun gawawwakin 'yan uwansu bayan ambaliya
Matan biyu, waɗanda dukansu matan aure ne ga mutum ɗaya, sun shafe mako guda suna kwana a waje tun lokacin da ambaliyar ruwa mafi muni da aka taɓa gani ta shafe garin, ta rusa gidajensu, ta kuma kashe sauran matan mijinsu biyu da yara 16.
Jama'ar Mokwa na ci gaba da fatan samun gawawwakin 'yan uwansu bayan ambaliya
Death toll in Nigeria floods rises to over 150 / Reuters
20 Yuni 2025

A cikin rana mai zafi a Mokwa da ke Nijeriya, Fatima da Habiba Jibrin suna zaune a ƙarƙashin itacen mangwaro, suna jiran dawowar gawawwakin da suke tsoron ba za a taɓa samun su ba.

Matan biyu, waɗanda dukansu matan aure ne ga mutum ɗaya, sun shafe mako guda suna kwana a waje tun lokacin da ambaliyar ruwa mafi muni da aka taɓa gani ta shafe garin, ta rusa gidajensu, ta kuma kashe sauran matan mijinsu biyu da yara 16.

Fatima, mai shekara 26, ta rasa yara huɗu, yayin da Habiba, mai shekara 27, ta rasa yara shida. Amma daga cikin mutane 18 da ake zaton sun mutu a dangin, gawawwaki huɗu kawai aka samu.

Labarin su – na kusan dukan dangi da aka shafe a safiya ɗaya – ya zama ruwan dare a Mokwa, a jihar Neja ta arewa ta tsakiya, inda adadin mutanen da aka tabbatar sun mutu ya tsaya a kusan 150, amma ana tsoron daruruwan mutane sun mutu – watakila fiye da adadin mutanen da suka mutu a duk faɗin ƙasar a shekarar 2024.

"Mun kasance muna kwana a waje ƙarƙashin itacen mangwaro da tabarma da kuma ragar sauro," in ji Fatima a tattaunawarta da kamfanin dillancin labarai na AFP. "Ko abinci ma, ba mu da shi."

Tun da gwamnati ba ta cika waiwayar wurin ba, suna dogaro ne kawai ga wasu mazauna garin da gidajensu ba su lalace ba. Mijinsu, malamin makarantar Islamiyya, yana fita kowace rana tun lokacin da ruwan ambaliya ya rusa gidaje fiye da 250 a al'ummar, yana neman sauran gawawwaki 14.

Fatan samun ƙarin gawawwaki

Aƙalla turakun wutar lantarki 15 ne suka lalace, wanda hakan ya jefa gari a cikin duhu.

Yanayin zafi ba ya bayar da sauƙi, kuma ruwa yana ƙaranci. Ana kuma tsoron cewa cutar kwalara – wadda ke yawaita bayan ambaliya – za ta ƙara jawo taɓarɓarewar wannan lamarin.

Masu aikin agaji da ƙungiyoyin bayar da agajin gaggawa sun gano gawawwaki har kusan kilomita 10 daga inda aka kwashe su zuwa Kogin Neja. Wasu mazauna garin sun shaida wa AFP cewa an gano wasu gawawwaki a wani ƙauye a jihar Kwara, wanda ke ke ɗayan tsallaken kogin.

Duk da haka, Fatima da Habiba suna ci gaba da fatan dawowar mijinsu kowace rana, ko da kuwa labari mara daɗi ne ya kawo.

"Za mu yi farin ciki idan ya iya samun gawawwakin su don mu yi musu jana'iza," in ji Fatima Jibrin.

Kamar su, Fatima Muhammed ma tana fatan a gano gawar ɗan jikanta, ko da kuwa a mace ne. Ta ce tana girka karin kumallo ne a safiyar ambaliyar lokacin da ta ga ruwa yana kwarara ta wata ƙaramar hanya a gaban gidanta.

Ba ta san cewa ruwan da ya taru tsawon kwanaki a bayan wani tsohon layin dogo domin fasa bangon laka. A cikin ƙasa da minti ɗaya, ruwan ya koma wani babban ambaliya mai ƙarfi.

Ta tsere ta bayan gida, kamar yadda ta shaida wa AFP, amma "jikanta ya bace yayin da yake ƙoƙarin bin ta."

Ta ce tana zaune tare da 'yarta kuma tana ganin kanta a matsayin nauyi. Amma har yanzu babu wani taimako da ya iso gare su.

Yawancin mazauna wannan al'ummar mai rinjayen Musulmi suna fushi cewa gwamnati ba ta bayar da isasshen taimako ba, yayin da Eid al-Adha ke gabatowa.

Mataimakin gwamnan jihar ya ziyarci wurin kuma ya yi alkawura, kuma gwamnati ta ce ta kawo kayan agaji. Amma da yawa daga cikin mazauna garin sun ce ba su ga komai ba.

A yayin da fushi ke ƙara yawa, wasu matasa sun yi barazanar dukan ɗan jaridar AFP, suna ɗaukar shi a matsayin jami'in gwamnati.

Yunkurin raba wasu kayan agaji ya ƙare ba zato ba tsammani a safiyar ranar bayan mazauna garin – waɗanda ba su yarda cewa ba wani shiri ne na ɗaukar hoto kawai ba – suka nace cewa a raba kayan a fili.

Uwargidan gwamnan, Fatima Mohammed Bago, ta kai ziyara ta gajeren lokaci zuwa wurin da abin ya shafa. Ba a ga jami'an gaggawa a wurin ba sai mintuna kaɗan kafin zuwanta. Sun bar wurin nan take bayan ta tafi.

Fatima da Habiba Jibrin, tare da Fatima Muhammed, sun ce ba ta zo wurinsu ba, kuma ba su samu wani taimako daga gwamnati ba.

"Ba abin da zan iya yi," in ji Mohammed Aliu, direban mota mai shekara 36, wanda ambaliyar ta kashe 'ya'yansa, matarsa da gidansa.

"Amma zan yi farin ciki idan zan iya ganin gawawwakin su."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us