Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Lakurawa ne sun kai hari a kauyen Kwalajiya da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a jihar Sokoto, inda suka kashe aƙalla mutum 15, a wani hari da mazauna yankin ke kallo a matsayin na ramuwar gayya ne.
Harin ya faru ne kimanin karfe 2:00 na ranar Talata, lokacin da jama’a ke gudanar da sallar Azahar.
Shaidu sun bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne gungu-gungu tare da buɗe wuta ba ƙaƙƙautawa inda suka harbi masu ibada a cikin masallaci da kuma manoma da ke gonakinsu.
Wani jagoran al’umma wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya bayyana cewa harin da aka kai, ramuwar gayya ce sakamakon kashe mambobin Lakurawa uku da aka yi a lokacin da maharan suka yi yunƙurin kai wani hari, kamar yadda jaridar Daily Trust a Nijeriya ta ruwaito.
“Wannan ne karo na farko da suka kai mana hari kai tsaye. Amma ina ganin ramuwar gayya ce saboda mutuwar mambobinsu uku,” in ji shi.
Wasu mazauna yankin sun kuma bayyana cewa maharan sun ƙona gonaki da gidaje da shaguna, duk da cewa basu cutar da mata ba a yayin harin. Sun lalata kayan abinci da aka adana a shaguna kafin su kona wasu gidaje.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce har yanzu ba a tantance adadin wadanda suka rasa rayukansu ba.
Sai dai wata majiya daga karamar hukumar Tangaza ta tabbatar da cewa mutane 15 ne suka mutu, yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon harbin bindiga kuma an kai su asibiti domin samun kulawa.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza tare da jami’an tsaro sun kai ziyara kauyen ranar Laraba domin halartar jana’izar wadanda suka mutu da kuma duba barnar da aka yi.