NIJERIYA
2 minti karatu
Saudiyya ta saki 'yan Nijeriya uku bayan tsare su tsawon watanni goma
Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta ce an samu nasarar sako 'yan ƙasar ne bayan tattaunawar diflomasiyya ta tsawon lokaci wanda hakan ya kai ga sallamarsu da kuma wanke su daga zarge-zargen da ake musu na safarar miyagun ƙwayoyi.
Saudiyya ta saki 'yan Nijeriya uku bayan tsare su tsawon watanni goma
Ko a shekarar 2019 sai da gwamnatin Nijeriyar ta yi ruwa ta yi tsaki aka sako wata matashiya mai suna Zainab Aliyu wadda Saudiyyar har ta kai ga yanke mata hukuncin kisa. / Hoto: Maitama Tuggar
5 Janairu 2025

Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta sanar da cewa Saudiyya ta saki wasu mata uku da ta kama a bara da laifin safarar miyagun ƙwayoyi.

An kama Hadiza Abba da Fatima Umate Malah da Fatima Kannai Gamboi ne tun a ranar 5 ga watan Maris ɗin 2024 a filin jirgin Mohammed bin Abdul Azeez da ke Madinah.

A cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Nijeriyar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an kama matan ne biyo bayan kamun wasu ‘yan Nijeriya biyu da aka yi da kafso 60 na hodar ibilis wanda nauyinsu ya kai gram 900.28 da kuma wasu kafso 70 na hodar ibilis ɗin da nauyinsu ya kai gram 789.5.

“Hukumomin Saudiyya sun tsare matan ne bisa zarginsu da hannu a taimakawa wurin safarar haramtattun kayayyakin da aka samu tare da ‘yan Nijeriyar da aka kama,” in ji sanarwar.

“An samu nasarar sako su ne bayan shafe tsawon lokaci ana tattaunawar diflomasiyya da shari’a, wanda hakan ya kai ga sallamarsu da kuma wanke su, da kuma mika su ga karamin ofishin jakadancin Nijeriya a Jedda,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Matan sun samu tarba daga Ambasada Muazam Nayaya, jakadan Nijeriya a ƙaramain ofishin jakdancin Nijeriya da ke kuma inda a halin yanzu ake jiran a kammala wasu shirye-shirye waɗanda suka shafi hukumar shige da fice domin su koma Nijeriya.

Ba wannan ne karo na farko da ‘yan Nijeriya ke faɗawa irin wannan tarkon ba a Saudiyya.

Ko a shekarar 2019 sai da gwamnatin Nijeriyar ta yi ruwa ta yi tsaki aka sako wata matashiya mai suna Zainab Aliyu wadda Saudiyyar har ta kai ga yanke mata hukuncin kisa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us