Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya yi gargaɗi cewa yaƙin Isra'ila a Gaza ya mayar da hannun agogo baya wajen ci gaban da aka samu a yankin tsawon shekaru, kuma hakan na iya haifar da matsaloli a duniya idan ba a dakatar da wannan farmaki ba.
“Idan ba a dakatar da farmakin Isra'ila da manufofin faɗaɗa yankinta ba, sakamakon zai shafi duniya baki daya,” in ji Hakan Fidan a ranar Lahadi yayin wani zama a taron shugabannin BRICS karo na 17 da aka gudanar a Rio de Janeiro, Brazil.
Da yake magana a wani taron tattaunawa mai taken “Karfin Hadin Kai, Harkokin Tattalin Arziki da Kudi, da Ƙirƙirarriyar Basira,” Fidan ya bayyana cewa ayyukan Isra'ila sun haifar da rikici ga hukumomin kasa da kasa da ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
“Rashin jin dadin al'ummar Falasdinawa yanzu ya zama ainihin abin da muke tattaunawa a kan batun hadin-kai,” in ji shi.
“Wannan yanayi babbar matsala ce ga sahihancin hukumomin da ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.”
Fidan ya bayyana cewa Turkiyya na kara kokari wajen tallafa wa warware rikicin cikin lumana da rage tashin hankali a yankin, kuma a shirye take ta goyi bayan zaman lafiya mai ɗorewa.
Ya kuma jaddada cewa dunƙulewar duniya ta kara zurfafa dangantakar juna, inda hakan ya sa sarkokin darajar kayayyaki, musamman a bangaren makamashi da ma'adanai masu muhimmanci, suka zama masu rauni. Ya yi kira da a mai da hankali kan ci gaba, samar da ayyukan yi, da cinikayya cikin 'yanci don cim ma ci gaba.
“Yayin da duniya ke tafiya zuwa tsarin da ba ya karkata ga bangare daya, jagorancin duniya kan fasahar wucin gadi ya zama babban fifiko,” in ji shi.
“Dole ne a dauki matakan da suka dace don hana fasahar wucin gadi zama sabon kayan mulki.”