Rundunar ‘yan sandan Nijeriya tare da haɗin gwiwar ‘yan sandan ƙasa da ƙasa na Interpol sun gano tare da mayar da motoci da dama da aka sace daga Nijeriya aka yi fasa-ƙwaurinsu zuwa ƙasashe maƙwabta.
Jami’an ‘yan sandan na Interpol sun gano wata mota ƙirar Toyota Prado (2020 model) a Accra babban birnin Ghana.
A sanarwar da ‘yan sandan Nijeriya suka fitar, motar ta wata ma’aikatar gwamnatin tarayyar Nijeriya ce inda aka ƙwace ta a lokacin fashi da makami a Abuja.
An kama mutum uku da ake zargi da fashin a Ghana kuma tuni aka kai su kotu a birnin na Accra.
Tuni aka mayar da motar Nijeriya inda aka miƙa ta ga ma’aikatar gwamnatin tarayyar.
Haka kuma jami’an na Interpol sun gano wata mota ƙirar Toyota Hilux (2018 model) mallakar wata ma’aikata ta Gwamnatin Nijeriya.
An sace motar ne a gundumar Utako da ke Abuja a ranar 18 ga watan Oktoban 2024.
Bayan bin diddiƙi da jami’an na Interpol suka yi, an gano motar a Agadez da ke Jamhuriyar Nijar inda jami’an na Interpol reshen Jamhuriyar Nijar suka miƙa motar ga wani babban ma’aikacin ma’aikatar ta Nijeriya a kan iyakar Nijeriya da Nijar.
Haka kuma a wani lamari mai kama da wannan, rundunar ‘yan sandan Nijeriyar ta ce tana aiki kan dawo da wasu ƙarin motoci biyu da aka sace a Abuja kuma aka sayar da su a Yamai babban birnin Nijar.