TURKIYYA
2 minti karatu
Shugaban Turkiyya ya aike da saƙon goyon baya ga Gaza da sauran inda ke fama da tashin hankali
Erdogan ya jaddada jajircewar Turkiyya wajen kawo ƙarshen tashin hankali a Falasɗinu da kuma tabbatar da cewa yaƙin da ake tsakanin Rasha da Ukraine ya zo ƙarshe da samar da zaman lafiya da adalci.
Shugaban Turkiyya ya aike da saƙon goyon baya ga Gaza da sauran inda ke fama da tashin hankali
Erdogan ya bayyana fatan cewa rashin zaman lafaiya a yankunan da tashin hankali ya shafa, ciki har da Gaza da Sudan da Somaliya zai nan gaba kaɗan / AA
5 Yuni 2025

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya miƙa saƙon gaisuwar Sallah ga dukkan Musulmai a faɗin Duniya, inda ya bayyana goyon bayansa ga Falasɗinawa da sauran al’ummomin da tashin hankali ya shafa a sassan duniya.

"A madadin ƙasata da al’ummata, cikin girmamawa ina gai da ‘yan’uwana maza da mata Falasɗinawa waɗanda ke tsayin-daka na mututaka bisa dukkan dabbancin Isra’ila da kuma waɗanda ke ƙaddamar da gwagwarmaya na jarumta a Gaza, da kuma sauran yankunan da aka mamaye," kamar yadda Erdogan ya bayyana a saƙonsa na bidiyo ranar Alhamis.

Ya kuma yaba wa waɗanda suka rasa rayukansu a Gaza, yana mai cewa: “Ina tunawa da dukkan ‘yan’uwanmu maza da mata a Gaza waɗanda suka yi shahada cikin waɗannan hare-haren da [Allah Ya yi musu] jinƙai, kuma ina fatan samun sauƙi cikin sauri ga waɗanda suka ji rauni.”

Erdogan ya bayyana fatan cewa tashin hankali a yankunan da rashin zaman lafiya ya shafa, ciki har da Gaza da Sudan da Somalia zai zo ƙarshe nan ba da jimawa ba.

"Mataki mai cike da tarihi wajen kawo ƙarshen yaƙin zubar da jini”

Ya tabbatar da jajircewar Turkiyya wajen kawo ƙarshen tashin hankali an Falasɗinu, yana mai cewa, “Muna yin dukkan abubuwan da muke da ikon yi wajen kawo ƙarshen kisan ƙare dangi a Falasɗinu da kuma tabbatar da cewa yaƙin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine ya zo ƙarshe da samar da zaman lafiya da adalci.”

Da yake magana game da ƙoƙarin diflomasiyya, Erdogan ya yi magana a kan wata ganawa da aka yi a Istanbul ranar Litinin 2 ga watan Yuni, wacce ya bayyana a matsayin "wani mataki mai cike da tarihi wajen kawo ƙarshen yaƙin na zubar da jini wanda a halin yanzu ya shiga shekararsa ta huɗu."

Da yake Magana game da ƙasar Siriya mai maƙwabtaka, Erdogan ya ce Turkiyya tana maraba da ƙoƙarin sabuwar  gwamnatin ƙasar kuma ya bayyana goyon baya ga burin Siriya na samun haɗin kan ƙasa da kare iyakokinta da kuma ci-gabanta na lokaci mai tsawo.

“Tare da goyon bayan ƙasashe ‘yan uwanmu a yankin, mun yi imanin cewa Siriya za ta cim ma zaman lafiya mai ɗorewa tare da sake samun martabarta ta da,” in ji shi.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us