NIJERIYA
2 minti karatu
Ana zargin wata ‘yar shekara 40 da yi wa yaro ɗan shekara 12 fyaɗe a Bauchi
Sanarwar rundunar ta ci gaba da cewa “Mutumin ya kai ƙarar matar wacce mazauniyar Tashan Jama’are ce, wadda ta ci zarafin yaron da ya kasance ta ɗauke shi aiki don taya ta sana’arta.
Ana zargin wata ‘yar shekara 40 da yi wa yaro ɗan shekara 12 fyaɗe a Bauchi
Kwamishinan 'yan sandan Bauchi / Nigeria Police
22 Afrilu 2025

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen jihar Bauchi ta ce ana zargin wata mata ‘yar shekara 40 da yi wa wani yaro ɗan shekara 12 fyaɗe a garin Azare.

“A ranar 1 ga watan Maris din 2025 ne wani ɗan ƙaramar hukumar Katagum ya kai rahoton wani mummunan abu da ya faru ga hedikwatar ‘yan sanda da ke Azare,” in ji sanarwar da rundunar ta wallafa a shafin Facebook ranar Talata 22 ga watan Afrilu, mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’arta
CSP Ahmed Mohammed Wakil.

Sanarwar ta ci gaba da cewa “Mutumin ya kai ƙarar matar wacce mazauniyar Tashan Jama’are ce, wadda ta ci zarafin yaron da ya kasance ta ɗauke shi aiki don taya ta sana’arta.

“Yaron wanda almajiri ne yana zama ne a gidan matar inda aka yi zargin ya shafe wata biyu yana fuskantar cin zarafi.”

A yayin da ake yi masa tambayoyi, yaron ya bayyana yadda matar, wacce ya ɗauka a matsayin uwa “ke cin zarafinsa”, musamman idan sauran mazaunan gidan ba sa nan, a cewar ‘yan sandan.

Sanarwar ‘yan sandan ta kuma ce yaron ya ba da labarin yadda ake ba shi wani lamurje da aka surka da wani abu duk sanda aka nufaci cin zarafinsa.

Ya kuma yi zargin cewa an sha cin zarafin nasa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba.

Matar ta amsa zargin da ake mata a lokacin da ake tuhumarta in ji ‘yan sanda.

Amma rundunar ta ce ana ci gaba da bincike, kuma da zarar an kammala, za a aika ta kotu don fuskantar shari’a.

 

 

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us