Xabi Alonso ya yi shelar sabon zamanin ne a lokacin da aka ayyana shi a hukumance a matsayin sabon kocin Real Madrid.
An naɗa Alonso, mai shekara 43, a matsayin kocin kulob ɗinsa na da a kan yarjejeniyar shekara uku ranar Lahadi inda ya maye Carlo Ancelotti – wanda zai ja ragamar tawagar ƙwallon ƙafa ta Brazil.
‘Yan Madrid sun yi fama da kaka mai wahala – inda suka sallama kofinsu na La Liga wa Barcelona, kuma suka sha kaye a hannun abokan gabansu a wasan ƙarshe na Gasar Copa del Rey da kuma Gasar Supercopa ta Sifaniya, kuma suka rikito daga Gasar Champions League a kararwarsu da Arsenal a matakin kusa da daf da na ƙarshe.
Amma a wani jawabin da ya gabatar a filin horswan Madrid mai suna Valdebebas ranar Litinin, Alonso ya ce: "[Wannan ] Farkon wani zamani ne."
Ya ƙara da cewa: "Magoya bayan Real Madrid sun ƙosa da a fara wannan sabon zamanin domin ci-gaba da kuma ƙara inganta tarihin wannan kulob ɗin.
"Wata muhimmiyar rana ce. Wata rana ce da zan sanya wa alama a kalanda har tsawon rayuwata. Na yi matuƙar murnar kasancewa a nan, inda na ke ji tamkar a gida nake."
Alonso, wanda ya lashe gasar lig da kuma kofi da Bayer Leverkusen a kakar 2023-24, ya bayyana matakin da ya ɗauka na komawa Madrid shekara 11 bayan ya bar kulob ɗin.
"Muna da ƙwararrun ‘yan wasan, muna da wani kulob ɗin da ke damar iya yin nasara nan gaba," in ji shi.
"Wannan ne ya ba ni dalilai masu yawa na zuwa nan da ƙwarin gwiwa da kuma fata mai yawa cewa zan iya samun sakamako mafi kyau daga ‘yan wasan tare da gina babban kulob.
"[Ina da] yaƙinin cewa za mu iya cim ma muhimman abubuwa, da suka dace da Real Madrid, da suka dace da dukkan waɗannan kofunan Turai ɗin, dukkan waɗannan nasarorinda aka samu cikin shekaru masu yawa,” in ji shi.