NIJERIYA
2 minti karatu
Wane ne sabon Shugaban APC, Nentawe Goshwe Yilwatda?
APC ta ce ta sanar da hakan a shafinta na X, bayan kammala taronta na Kwmaitin Koli karo na 14.
Wane ne sabon Shugaban APC, Nentawe Goshwe Yilwatda?
Farfesa Nentawe / Others
24 Yuli 2025

Ministan Jinƙai da Rage Talauci na Nijeriya, , Nentawe Yilwatda ya zama sabon shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, bayan zaɓarsa da mambobin Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar suka yi a ranar Alhamis.

APC ta ce ta sanar da hakan a shafinta na X, bayan kammala taronta na Kwmaitin Koli karo na 14.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma ne ya fara gabatar da son a zaɓe shi a matsayi, sai kuma shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajudeen ya goya wa hakan baya.

Daga nan ne sai aka sanar da ƙudurin inda sauran mutane suka nuna amincewa kuma aka tabbatar da shi.

Wane ne Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda?

An haifi Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, wanda ɗan siyasa ne daga jihar Filato, a watan Agustan 1968.

Injiniya ne, kuma masanin ilimi wanda a yanzu shi ne Ministan Ayyukan Jinkai da Yaki da Talauci na Nijeriya, bayan naɗin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa a watan Oktoban 2024.

Nentawe ya kasance dan takarar jam’iyyarsa ta APC a zaben gwamna na 2023 a jihar Filato.

Ya taba rike mukamai kamar kwamishinan zabe a jihar Benue, da kuma daraktan ICT a Jami'ar Aikin Gona ta Tarayya ta Makurdi, tsawon shekaru 12.

An naɗa Nentawe a matsayin mai kula da harkokin kamfen na takarar Tinubu/Shettima a Jihar Filato a lokacin zaɓukan 2023

Ya yi takarar gwamnan jihar Filato a 2023 amma ya sha kaye a hannun ɗan takarar PDP, inda ya kai ƙara kotu amma bai yi nasara ba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us