NIJERIYA
2 minti karatu
‘Yan sanda sun kama wata mace ‘mai safarar makamai da miyagun ƙwayoyi’ ga ‘yan ta’adda
Matar, wadda rundunar ‘yan sanda ta kama ta tun a watan Disamban 2024, ta shaida wa rundunar cewa “wani mutum ne ya aike ta ta kai makaman jihar Katsina.”
‘Yan sanda sun kama wata mace ‘mai safarar makamai da miyagun ƙwayoyi’ ga ‘yan ta’adda
Matar, wadda rundunar ‘yan sanda ta kama ta tun a watan Disamban 2024, ta shaida wa rundunar cewa “wani mutum ne ya aike ta ta kai makaman jihar Katsina.” / Nigeria Police
18 Maris 2025

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ta samu nasarar kama wata mata da ‘mai safarar makamai da miyagun ƙwayoyi’ ga ‘yan ta’adda a ƙoƙarinta na kai kayayyakin jihar Katsina daga ƙauyen Doro a kan titin Keffi zuwa Abuja.

A sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Talata mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a Olumuyiwa Adejobi, ta ce an kama matar mai shekara 30 da kayayyakin da suka haɗa da jigidar harsasai 124 da aka ƙunshe a cikin wata jarkar man-ja mai cin lita biyar.

Matar, wadda rundunar ‘yan sanda ta kama ta tun a watan Disamban 2024, ta shaida wa rundunar cewa “wani mutum ne ya aike ta ta kai makaman jihar Katsina.”

Binciken da aka ƙara yi ya gano wasu da dama da ke da hannu a lamarin kuma an kai ga kama su.

A wani ci gaban mai kama da haka, rundunar ‘yan sandan ta ce a wani samame da aka yi a ranar 1 ga Fabrairun 2025, jami’an rundunar FID-STS, da ke aiki kan sahihan bayanan sirri, sun kama wani mutum mai suna Alhaji Usman Yahaya mai shekara 50, da Joseph Matthew mai shekara 27 da Solomon Bala mai shekara 25, dukkansu mazauna garin Postiskum na jihar Yobe.

An kama su ne a lokacin da suke safarar kwali guda 30 na maganin codeine da sauran magunguna daban-daban a kusa da Postiskum.

Sun yi ikirari cewa za su kai magungunan ne domin a kai wa ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram, da masu garkuwa da mutane da ke addabar jihar Yobe da maƙwabtanta.

Bugu da ƙari, a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, jami’an FID-STS, sun kama ƙarin mutum uku da bindigogin AK-47 guda 10. Wadanda ake zargin da aka yi musu tambayoyi sun amsa laifinsu da hannu a cinikin makamai, inda suka karbi kudi Naira N3,980,000 a biyan karshe na makaman da ya kamata su yi ciniki da su.

Rundunar ta ce waɗannan nasarori suna cikin na baya bayan nan da ta samu wajen daƙile miyagun laifuka da ayyukan ta’addanci da suka hada da fasa-ƙwauri da safarar ƙwayoyi da na jabun kuɗi.

Ta kuma yi kira ga ‘yan kasa da su yi taka-tsan-tsan, su kuma kula da irin ta’addancin wadannan masu fasa-kwauri, tare da yin kira ga “a kai rahoton duk wasu kai-kawo na rashin gaskiya cikin gaggawa ga hukumomin da suka dace.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us