Matashin tauraron ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal mai shekaru 17, ya ƙara samun wata babbar lambar yabo a rayuwarsa ta wasa, inda ya lashe kyautar Laureus World Breakthrough of the Year a Gasar Laureus World Sports Awards ta shekarar 2025.
Yamal ya zama ɗan wasa mai tasiri ga Barcelona da kuma tawagar ƙasarsa Sifaniya, bayan kakar wasa mai tagomashi a ƙungiyarsa, inda ya zura ƙwallaye 6 da tallafin ƙwallo 12 a La Liga.
A gasar Zakarun Turai ma, Yamal ya ci ƙwallaye 3. Kuma ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da Sifaniya ta samu a gasar UEFA European Championship, inda aka karrama shi da lambar yabo ta Matashin Ɗan Wasa na Gasar.
Sai dai Yamal bai samu damar halartar bikin na Laureus Awards, sakamakon wasan La Liga da Barcelona za ta kara da RCD Mallorca, wanda za a yi cikin ƙasa da awa 24 bayan bikin bayar da kyaututtukan a birnin Madrid a daren Litinin.
Lamine Yamal ya miƙa saƙon godiyarsa ta hanyar saƙon bidiyo.
Saƙon godiya
Lamine ya faɗa a saƙonsa cewa, “Barka da yamma, kowa da kowa. Na so kasancewa tare da ku amma hakan bai yiwu ba. Da farko, ina so in gode wa Laureus Academy saboda wannan kyautar. Wannan babbar girmamawa ce gare ni da iyalaina.”
Kyautar Laureus tana karrama bajintar a fagen wasanni a fannoni daban-daban. An zaɓi Yamal daga jerin sunayen waɗanda suka cancanta da suka haɗa da Julien Alfred (wasannin motsa-jiki), Summer McIntosh (ninƙaya), Letsile Tebogo (wasannin motsa-jiki), Victor Wembanyama (ƙwallon kwando), da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jamus, Bayer Leverkusen.
Shahararriyar ‘yar wasan motsa-jiki Ba’amurkiya, Simone Biles, ita ce ta lashe lambar yabo ta ‘Yar Wasa ta Shekara.