NIJERIYA
2 minti karatu
Ganduje ya sauka daga shugabancin Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya
Majiyoyi daga uwar jam’iyyar ta APC a Abuja da kuma wasu na kusa da tsohon shugaban sun tabbatar wa da TRT Afirka Hausa matakin, duk da cewa har lokacin haɗa wannan rahoton ba a fitar da sanarwa a hukumance ba.
Ganduje ya sauka daga shugabancin Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya
Abdullahi Umar Ganduje / All Progressive Congress
27 Yuni 2025

Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugabancin jam’iyyar nan-take a ranar Juma’ar nan.

Majiyoyi daga uwar jam’iyyar ta APC a Abuja da kuma wasu na kusa da tsohon shugabannin sun tabbatar wa da TRT Afrika Hausa matakin, duk da cewa har lokacin haɗa wannan rahoton ba a fitar da sanarwa a hukumance ba.

Sai dai har yanzu babu ƙarin bayani kan dalilan ajiye aikin da Gandjuje ya yi, sai dai wasu majiyoyin na cewa ya sauka ne saboda dalilai na “rashin lafiya.”

Zuwa yanzu ba a san wane ne zai maye gurbin Ganduje a matakin na shugabancin APC ba.

Dama dai an jima ‘yan APC daga yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya suna neman a mayar musu da shugabancin jam’iyyar mai mulkin Nijeriya, kasancewar wanda Ganduje ya gada ya fito ne daga yankin.

A watan Agustan 2023 ne aka naɗa tsohon gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje shugabancin APC a matsayin riƙo, bayan ajiye aiki da tsohon shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya yi, ‘yan watanni bayan rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya.

Ganduje dai na daga na gaba-gaba wajen goyon bayan takarar Bola Tinubu ta shugabancin Nijeriya tun kafin a kai ga zaɓen fitar da gwani na

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us