Zaman lafiya a duniya na bukatar fahimtar kowa a duniyar bisa gaskiya da adalci, in ji shugaban sadarwa na Turkiyya.
Fahrettin Altun ya ce, "Domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa tushen gaskiya da adalci su tabbata a duniya," in ji Fahrettin Altun yayin taron manema labarai na Turkiyya da China da cibiyar sadarwa ta Turkiyya ta shirya a Ankara babban birnin kasar a ranar Laraba.
Altun ya jaddada cewa, a tarihi, dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da China ta dogara ne kan mutunta juna, da hadin gwiwa, da kusancin al'adu.
Turkiyya na ƙoƙarin samar das zaman lafiya da cigaba
Altun ya lura cewa, "Turkiyya tana gwagwarmayar samar da zaman lafiya da wadata ga kowa da kowa da dukkan karfinta."
Ya kara da cewa, "Da wannan hangen nesa, kasarmu ta dauki nauyin sasanta kusan dukkanin rikice-rikice na baya ayan nan da kuma daukar nauyin tarurrukan diflomasiyya da shawarwarin zaman lafiya. Babban burinmu shi ne tabbatar da gaskiya da adalci a kowane fanni."
"Hanyar yin hakan ita ce tabbatar da samar da kyakkyawan wakilci a tsarin sadarwar kasa da kasa da kuma harkokin diflomasiyya."
Altun ya kara da cewa, tsarin watsa labarai na duniya da ke jure wa bayanai inda duk mutane za su sa a ji amonsa, shi ma mabudin zaman lafiya ne a duniya.
Labaran ƙarya sun zama matsala ta ruwan-dare
Altun ya ce sabbin fasahohin sadarwa, irin su na’ura mai kwakwalwa, sun yi tasiri sosai a kafafen yada labarai; duk da haka, ya kara da cewa, wannan sauyin ya kuma kawo kalubale.
"Musamman barazana irin su labaran ƙarya da ayyukan fahimta da sarrafa labarai ta hanyar amfani da ƙirƙirarriyar basira, duk sun zama matsaloli na duniya ba na yanki ɗaya ba kawai," in ji shi.
Ya jaddada mahimmancin ba da fifiko ga tabbatar da gaskiya a fannin sadarwa, daidaito kan bayanai, kuma kafofin watsa labarai su tabbatar ba a lalata gaskiya ba.
"Hanyar yin hakan ita ce ta hanyar hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, da musayar gogewa, da hadin kan kafofin watsa labaru na kasa da kasa," in ji Altun.
Ya kara da cewa, "Saboda haka, muna raya Dandalin Watsa Labarai na Turkiyya da China a matsayin wani dandali mai amfani da moriyar bai daya ba na kasashen biyu ba kawai, har ma da al'ummomin duniya baki daya."
Altun ya kara da cewa, a ko da yaushe suna ba da fifiko da kuma kimar musayar gogewa da bayanai da ƙasashe masu manyan dabaru, kamar China.
Ya kara da cewa, wannan dandalin wata alama ce ta fahimtar juna, inda ya kara da cewa, Turkiyya da China kasashe biyu ne da ke da karfin bunkasa ba kawai a fannin tattalin arziki ba, har ma da hadin gwiwa bisa wayewar kai.