NIJERIYA
1 minti karatu
An kashe ɓarayin daji da sojoji a Jihohin Neja da Kaduna
Cikin ‘yan makonnin nan dai ana samun yawan hare-haren ‘yan ta’adda kan sansanonin soji musamman a arewa maso gabashin Nijeriya.
An kashe ɓarayin daji da sojoji a Jihohin Neja da Kaduna
Sanarwar dai ba ta faɗi adadin sojojin da aka kashe ba / Nigerian army
25 Yuni 2025

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe gomman ‘yan bindiga a Kwanar Dutse Mairiga da Boka a jihar Neja da kuma Aungwan Turai a ƙaramar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna.

Wata sanarwar da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Laraba ta ce lamarin ya auku ne ranar Talata a lokacin da ‘yan bindiga suka far ma sansanonin sojojinta ta hanyoyi uku.

Sojoji sun mayar da martani ga harin ‘yan bindigar da hare-hare ta sama da ƙasa lamarin da ya kashe gomman ‘yan bindigar, in ji sanarwar sojin Nijeriya.

Sai dai, wasu [sojoji] jarumai sun rasa rayukansu a arangamar da aka yini ana yi yayin da huɗu daga cikinsu suka ji rauni kuma a halin yanzu suna samun maganin ciwon harbin bindiga da suka ji,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa nan gaba rundunar za ta ƙara bayani game da lamarin.

Cikin ‘yan makonnin nan dai ana samun yawan hare-haren ‘yan ta’adda kan sansanonin soji musamman a arewa maso gabashin Nijeriya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us