Kyaftin din Manchester United Bruno Fernandes ya ƙi amincewa da shirin komawa kulob din Al Hilal na Saudiyya saboda ‘‘yana son ya taka leda a wani babban mataki da ya dace.’’
Fernandes ya tabbatar da hakan ne a ranar Talata inda ya ce, ya sami " tayi mai gwaɓi" daga kulob din da ke Riyadh don ya koma can bayan rashin karsashin kaka da United ta samu.
"Sun jira na in yi tunani game da makomata, saboda na ce kawai idan har Manchester ta yi nazarin cewa lokaci ya yi da zan ci gaba, zan ba da hadin kai" kamar yadda fassarar kamalan Fernandes suka bayyana.
"Na yi magana da Ruben Amorim, kuma a lokacin ya ce min kar na tafi, sai na yi magana da Man United, suka ce ba sa so su sayar da ni. Idan ina son tafiya, zan iya, amma ba sa bukatar kudin, kuma ba sa son su sayar da ni’’ in ji shi.
Tayin Fam miliyan 100
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun nuna cewa Al Hilal ta shirya biyan fam miliyan 100 (dala miliyan 135) don daukar Fernandes mai shekaru 30 daga United yayin da za a na ba shi albashin fam 700,000 ($ 946,000) a kowane mako don buga wasa a ƙungiyar Saudi Pro League.
"Wannan tayi ne mai ban sha'awa," in ji Fernandes. "Shugaban Al Hilal, ya mutunta ni sosai, ya yi magana da manajana, amma sai na yi magana da matata, kuma a matsayinmu na iyali, muna son ganin abin da nake so in yi, sai ta tambaye ni, me kake son yi da makomarka?"
A bara Fernandes ya rattaba hannu kan kwantiragin ci gaba da zama a Old Trafford har zuwa Yuni 2027.
Wannan kakar dai ba ta tafi kamar yadda aka tsara ba, domin Red Devils ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai bayan da ta kare a mataki na 15 a gasar ta Premier, yayin da kuma ta shiga cikin kunci na rashin nasarar da ta yi a wasan karshe na gasar Europa a hannun Tottenham.