TURKIYYA
1 minti karatu
Jirgin ruwan Turkiyya mai sarrafa gas na farko ya isa tashar ruwa da ke Gaɓar Tekun Bahar Aswad
Ana sa ran jirgin ruwan zai ninka adadin gas ɗin da ake samarwa a Tekun Bahar Aswad zuwa cubic meter miliyan 20, sannan kuma ana sa ran ya biya buƙatun kimanin gidaje miliyan takwas a Turkiyya da ke buƙatar gas.
Jirgin ruwan Turkiyya mai sarrafa gas na farko ya isa tashar ruwa da ke Gaɓar Tekun Bahar Aswad
Ana sa ran jirgin ruwan zai shafe shekara 20 yana aiki a wurin / AA
31 Mayu 2025

Turkiyya ta ƙaddamar da jirgin ruwa na farko da ke sarrafa iskar gas mai suna Osman Gazi inda jirgin a ranar Asabar ya isa tashar ruwa ta Filyos da ke Zonguldak ta Turkiyya da ke Gaɓar Bahar Aswad.

An ƙaddamar da katafaren jirgin ruwan ne a Fadar Shugaban Ƙasa ta Dolmabace a birnin Istanbul a ranar 29 ga Mayu – a lokacin cika shekara 572 da ƙwace Istanbul – a yayin wani biki da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya halarta da kuma ministan makamashi da albarkatun ƙasa na Turkiyya inda jirgin ya ratsa ta mashigar ruwan Istanbul.

Jirgin zai iya samar da iskar gas wadda ta kai cubic meter miliyan 10.5 a rana guda da kuma raba gas ɗin da ya kai cubic meter miliyan 10.

Ana sa ran wannan jirgin ruwan zai ƙara adadin gas ɗin da ake samarwa a Tekun Bahar Aswad zuwa cubic meter milian 20 a kullum.

Jirgin ruwan wanda ke iya ɗaukar ma’aikata 140, na da tsawon meter 298.5 da kuma faɗin meter 56, sai kuma zurfin meter 29, ana kuma sa ran zai fara aiki a tsakiyar shekarar 2026.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us