Nijeriya
2 minti karatu
‘Yan sanda a Bauchi sun kama matar da ake zargi da shaƙe kishiyarta har lahira
Bayan aika kishiyarta lahira, sai ta zuba mata ruwan zafi da kuma ƙona jikinta da buhun da aka cinna wa wuta domin yin rufa-rufa, kamar yadda binciken ‘yan sanda ya bayyana game da wadda ake zargin
‘Yan sanda a Bauchi sun kama matar da ake zargi da shaƙe kishiyarta har lahira
Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan an zargi wani mutum da kashe matarsa a Jihar Bauchin kan abincin buɗa-baki.
21 orë më parë

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Bauchi ta kama wata mata bisa zargin kashe kishiyarta a Bauchi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Bauchi Ahmed Wakil ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar inda ya ce an kama Fatima Mohammed mai shekara 28 kan zargin shaƙe kishiyarta mai suna Hajara Isa har lahira.

Ya bayyana cewa mijin matan biyu wato Sale Isa ne ya kawo musu rahoton faruwar lamarin a ranar 3 ga watan Maris ɗin 2025 inda ya ce wa ‘yan sanda yana shakku game da yadda matarsa ta rasu.

 “A ranar 3 ga watan Maris ɗin 2025, da misalin 8:00 na safe, wani Sale Isa daga Anguwan Sarakuna da ke Bauchi ya kawo rahoto game da yadda matarsa ta mutu. Iyalansa sun yi zargin cewa suna ganin kishiyarta na da hannu a mutuwar,” in ji sanarwar.

 “Binciken wucin-gadi da aka gudanar ya nuna Fatima Mohammed na da hannu a mutuwar Hajara. A lokacin da ake mata tambayoyi, ta bayyana cewa ta shaƙe ta ne har ta mutu. A yunƙurinta na ɓoye abin da ya faru sai ta zuba mata ruwan zafi da kuma ƙona jikinta da buhun da aka cinna wa wuta,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan an zargi wani mutum da kashe matarsa a Jihar Bauchin kan abincin buɗa-baki.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us