SIYASA
2 minti karatu
‘Yan sandan Kano na bincike kan musabbabin rikici tsakanin magoya bayan Aminu Bayero da Sanusi na II
An samu arangama tsakanin magoya bayan tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da na Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
‘Yan sandan Kano na bincike kan musabbabin rikici tsakanin magoya bayan Aminu Bayero da Sanusi na II
Kofar Kudu a Masarautar Kano / Reuters
10 Yuli 2025

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta kafa kwamitin mutum takwas domin binciken musabbabin rikici tsakanin magoya bayan Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano Ibrahim Bakori ne ya sanar da hakan a ranar Laraba a ofishinsa a lokacin da ya karɓi baƙuncin Wakilan Kafafen Watsa Labarai a jihar.

Ya ce kwamitin zai yi aiki tare da miƙa rahotonsa cikin kwanaki bakwai.

Me ya faru tsakanin bangarorin biyu

Tuni dai rundunar ‘yan sandan ta Kano ta sanar da kama mutane huɗu da ke zargi da hannu a rikicin da ya afku a ranar Lahadin da ta gabata a Ƙofar Kudu, fadar Masarautar Kano.

Kakakin ‘yan sandan Kano Abdullahi Kiyawa ya sanar da manema labarai cewa sun kama mutane huɗu, kuma suna ci gaba da riƙe su har sai an kammala bincike.

An samu arangama tsakanin magoya bayan tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da na Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

‘Yaran tsohon Sarki Bayero sun karya ƙofar Gidan Rumfa’

Tun da fari, kwamitin yaɗa labarai na Masarautar Kano ƙarƙashin Sadam Yakasai ya fitar da sanarwar cewa wasu da ake zargin magoya bayan Alhaji Aminu Ado Bayero ne suka kai wa gidan Rumfa hari.

A sanarwar da suka fitar, sun zargi magoya bayan Bayero da cewa “Sun karya ƙofar shiga tare da kai hari kan dogarai, sun jikkata wasu daga ciki. Sun lalata motocin ‘yan sanda da ke fadar.”

Ɓangaren Sarki Sanusi II ya yi zargin cewa da gangan tawagar tsohon Sarki Aminu Ado Bayero ta wuce ta gaban Gidan Rumfa da ke Ƙofar Kudu, maimakon su bi hanyar da ta kamata daga Ƙoƙi zuwa Gidan Nassarawa.

‘Magoya bayana sun kare kansu ne’

Ɓangaren Sarkin Kano Bayero ya bayyana cewa a lokacin da suke wucewa ta kusa da gidan Rumfa, babu wanda ke ɗauke da makami, amma dole aka tilasta musu kare kansu.

Mai Magana da yawun Sarkin Khalid Uba ya ce “Bayan mun je gaisuwar ta’aziyya gidan Dantata, da muka isa Kofar kudu sai wasu suka tare hanya da duwatsu da makamai a Kofar Kudu.”

Uba ya ƙara da cewa, sakamakon jifan su da duwatsu, dole ta sanya su kare kai inda suka samu nasarar kora su cikin gidan sarkin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us