Manufar harkokin wajen Amurka kan yakin Rasha-Ukraine a sauya sosai tun bayan dawowar Trump fadar White House a farkon shekarar nan.
Dakatar da bawa Ukraine tallafin soji da Amurka ta yi da daina musayar bayanan sirri da Washington ta yi da Kiev su zo da babbar damuwa game da kasar ta Gabashin Turai kan ikon ci gaba da yaki da Rasha.
Gwamnatin shugaba Vladimir Putin a yanzu ta shiga tsaka mai wuya inda ake matsa mata lamba kan ta tattauna da sulhuntawa da Moscow.
A ranar 4 ga Maris, Zelensky ya ce “Ukraine a shirye ta ke da ta zauna ateburin sulhu” kuma “ni da tawagata mun shirya aiki da shugabancin Trump don samun dauwamammen zaman lafiya”.
Yarjejeniyar da za ta bawa Moscow damar mamaye wani yankin Ukraine da ke karkashin ikonta a yanzu haka, tare da janye wani bangare na rage takunkuman tattalin arziki, zai zama abinda Cremlin ke bukata.
Idan aka samu irin wannan sakamako, to za a faranta wa shugaban Rasha Vladimir Putin shekaru uku bayan kaddamar ‘farmakan soji na musamman” a wasu bangarorin Ukraine.
Wata tambaya mai muhimmanci ita ce; ta yaya dakatar da yakin Ukraine da sharuddan da za su amfani Rasha zai sauya kimar Rasha a kasashen Larabawa?
A yayin da Rasha ta kara yawan kai agajin soji kai tsaye a Syria shekaru goman da suka wuce don karfafa wa gwamnatin Assad, wanda a lokacin take rike da iko da kashi 20 na fadin kasar Syria, Moscow sun tura sako mai karfi ga dukkan gwamnatoci a duniyar Larabawa da ma sauran yankunan.
Babban abin fahimta shi ne taimakon soji daga Rasha na iya hana gwamnati faduwa.
Wannan samar da kima ga Rasha a matsayin mai taka rawa a duniya da ke kalubalantar Amurka, wadda ta fuskanci Gabas ta Tsakiya da halayyar da kasashen Larabawa da dama suka yi wa kallon mai hatsari da janyo rikici saboda afka wa Iraki a 2003 da irin martanin da ta mayar bayan boren kasashen Larabawa, musamman a Masar, a 2011.
A takaice, rawar da Moscow ta taka a Syria a tsakanin 2015 da 2016 ta taimaka wajen rufe wani babi na tarihi inda kasahsen Larabawa - da wasu da dama fadin duniya, ciki har da kasashen Yamma - na iya kallon Rasha a matsayin mai rauni ko mara muhimmanci a lokacin bayan yakin cacar - Baki.
Amma bayan kaddamar da “farmakan musamman na soji” a Ukraine, Rasha ta fuakanci matsaloli da dama a filin daga da suka bakantar da kimar Moscow a idanuwan kasashe. Gazawar ta na samun cikakkiyar nasara kan ‘yar karamar kasa makociya ya sany kasashen Larabawa sauya tunani game da Rasha din da suka yi wa fahimta ta daban a lokacin kai duki Syria a 2015 da 2016.
Za kuma a iya cewa an bukaci shugabannin Larabawa a wannan lokaci da su duba idan karfin sojojin Moscow na gake ne ko kawai damsar takarda ce.
Duk da babu wata kasar Larabawa da ta dauki matakin kalubalantar Rasha, kuma babu wadda ta yanke hulda da Moscow, yakin Ukraine ya sanya kasashen Larabawa tsintar kansu a halin rashin ganin dalilin da zai sanya su juya wa Cremlin baya saboda dalilai na tsaro.
Yakin Ukraine, a yayin da ya ta’azzara, ya zama abin baiwa fifiko daga Rasha a fagen kasa da kasa. Syria kasa ce ta Larabawa da ta dogar kan Rasha a matsayin garanton tsaro, kuma Moscow ta bayar da fifiko ga yakin Ukraine sama da komai wanda hakan ya sanya ta barin Syria baki daya.
Wannan dalili da ma wasun su, ya bayar da gudunmawa sosai wajen rugujewar gwamnatin Assad a shekarar da ta gabata, wanda ya sanya kasashen Larabawa fara tantamar ko Rasha za ta zama kawarsu ta tsaro a nan gaba.
A yanzu, idan ‘yan kasar Rasha suka kulla yarjejeniya a Ukraine da za ta faranta musu aka kuma dakatar da yakin, to Moscow na iya nutsuwa ta dawo da hankalinta zuwa Gabas ta Tsakiya. A yayin hakan, kasashen Larabawa na iya auna cewa wannan zai zama lokacin kulla alka mai karfi da Moscow.
Yakin Ukraine ya jefa Rasha cikin babbar matsin lambar tattalin arziki, wanda ya sanya dole Rasha sauya akala daga cika sharuddan kulla yarjejeniyar sayar da makamai da kasashen waje.
Amma kuma, a baya bayan nan Aljeriya ce kasar waje ta farko da ta fara sayen jirgin yaki samfurin Sukhoi Su-57E, kuma abin duba wa ne ko sauran kasashen Larabawa ma za su bi sahun Aljeriya wajen zurfafa alakar soji da Rasha bayan yakin Ukraine da kuma canye mata takunkumai.
Koma ta yaya ne, yadda yakin Ukraine ya afku da abin da ya bari, dayadda ya zama silar karyewar gwamnatin Assad, zai iya zama dalilin da zai sanya kasashen Larabawa yi wa Moscow wani kallo na daban a tsawon lokaci.
Dakatar da yakin kadai ba zai kawar da shakkun a ake na ikon rasha ta zama kawa a sha’anin tsaro ba. Babban darasin da kasashen Larabawa suka dauka kan Syria shi ne yadda Assad ya dogara kacokan kan Moscow wanda hakan ya zama mai hatsari.
A karshe, kasashen Larabawa da suka dogara dungurungum kan Amurka a sha’anin tsaro za su karya gada su hada kai da Moscow a yanzu.
Duk da haka, kasashen Larabawa irin su hadaddiyar Daular Larabawa, Sudiyya, masar, da ma Syria bayan Assad za su kalli alakarsu da Rasha a matsyin mai biyan bukatar kasashensu ta lokaci mai tsayi.
Baya ga haka, da yawa daga wadannan kasashe sun gaji da manufofin kasashen waje na Amurka.
Kalaman trump na ‘tsaftacewa’ a Gaza ya girgiza shugabannin Larabawa da ke kallon wannan shiri a matsayin na murkushe kabilu da kashe su wanda zai kuma tirsasa raba mutane miliyan 2.2 su rasa matsugunansu, wanda hakan zai sake ta’azzara yanayi tsaro da zaman lafiya a Falasdin.
Wannan shiri da ba shi da tabbas, idan har za a ce a aiwatar da shi, kai tsaye zai shafi zaman lafiya da kwanciyar hankalin Masar da Jirdan - manyan kawayen Amurka a gabas ta Tsakiya.
Sannan kuma kasashen Larabawa sun ga manufar Trump ga makomar Gaza, da cewa ya fi bayar da fifiko ga masu tsaurin ra’ayi na Isra’ila maimakon bukatar kasashen Larabawa na wanzar da zaman lafiya.
Ba sai an ce wani abu ba game da goyon bayan da gwamnatin Biden ta baiwa Isra’ila a lokacin a ake tsaka da yaki a Gaza.
Da yadda kasashen Larabawa da dama ke kallon Amurka a matsayin kawar da ba za a dogara a kanta ba saboda ta gaza fahimtar damuwarsu ta tsaro, manyan kasashen duniya irin su Rasha da ke goyon bayan warware rikicin ta hanyar kafa kasashe biyu Isra’ila-Falasdinu, su ne wadanda shugabannin Larabawa a wani lokacin suke kallo a matsayin na dama-dama.
A wannan yanayi na bangarori daban-daban, shugabannin Larabawa za su kalli Rasha a matsayin jigo guda, inda China da India ma wasu jigogin ne.
Kasashen Larabawa da Rasha na amfanar juna a dangantakarsu, kuma shugabanni a duniyar Larabawa za su ci gaba da mu’amala da gwamnatin Putin don samun tafiya a kan hanyar Rasha a balaguro mai hanyoyi da dama da suke yi.
Dakatar da yakin Ukraine bisa sharuddan da za su bayyana Rasha ce ta yi nasara na iya kawo ra’ayi karbabbe a tsakanin kasashen jagororin Larabawa da jami’an tsaro cewa Moscow babbar jaruma ce da ya kamata a yi mu’amala da ita, a yayin da su kasashen ke neman ‘yancin rabuwa da Amurka.