WASANNI
2 minti karatu
Wa zai zama gwarzon shekara na gasar Firimiya: Fernandes, Isak, Palmer, Rice, MacAllister ko Salah?
'Yan wasa shida a Ingila na takarar zama gwarzon ɗan ƙwallon shekara na gasar Firimiya ta Ingila.
Wa zai zama gwarzon shekara na gasar Firimiya: Fernandes, Isak, Palmer, Rice, MacAllister ko Salah?
/ Reuters
20 Yuni 2025

An fitar da jerin taurarin ‘yan was shida da za a zaɓi gwarzon shekara na gasar Firimiya ta Ingila a bana daga cikinsu.

Cikin zaratan ‘yan wasan akwai ‘yan Liverpool biyu, wadda ita ce ƙungiyar da ta ɗaga kofin gasar Firimiya na bana, wato Mohamed Salah da Alexis Mac Allister.

Sauran ‘yan wasan su ne Bruno Fernandes na Manchester United, da Alexander Isak na New Castle, da Cole Palmer Chelsea, da kuma Declan Rice na Arsenal.

Takwarorin ‘yan wasan ne suka zaɓo taurarin shida da suka nuna bajinta a kakar wasan da aka kammala watan jiya.

Salah ne gwarzon ƙungiyar marubuta

Tun a Mayu ne aka zaɓi Mohamed Salah a matsayin gwarzon ɗan wasan ƙwallo na maza na shekara, ƙarƙashin Ƙungiyar ‘Yan Jarida Marubuta Wasannin Kwallon Ƙafa ta Ingila.

Salah ya zama ɗan wasa na farko da ya samu lambar yabon har karo uku, wato a 2018, 2022, da 2025. Kuma ana ganin shi ne kan gaba wajen damar lashe gwarzon ɗan wasa na hukumar FA.

Zaƙaƙurin ɗan wasan ya kammala kakar bana ne da cin ƙwallaye 29 da tallafin ƙwallo 18, wadda yake nufin akwai hannunsa a cin ƙwallaye 47.

Shi ne ya lashe Takalmin Zinare na kakar, bayan da ya buga duka wasanni 38 da Liverpool ta buga a kakar ta bana.

Sai a ranar 19 ga Agusta ne da za a sanar da wanda ya lashe kyautar ta bana a wani biki da za a yi a Manchester.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us