Gidauniyar Maarif ta Turkiyya ta shirya babban bikin yaye dalibai na kasa da kasa daga kasashe 10 na Afirka, wadanda suka kammala karatunsu na jami'a a Turkiyya.
Gidauniyar tana aiki ne don bunkasa ilimi, ciki har da bayar da tallafin karatu ga daliban kasashen waje da gudanar da makarantu a kasashe da dama, a matsayin wani bangare na ƙudirin Turkiyya na karfafa dangantaka da kuma inganta ilimi a duniya.
Maimakon jefa hular kammala karatu sama kamar yadda aka saba, daliban Maarif sun yi bikin yaye su ta hanyar harba jiragen takarda masu launin tutar Falasdinu, a matsayin nuna goyon baya ga Falasdinu yayin da Isra'ila ke ci gaba da yaƙinta da Gaza.
Fiye da dalibai 100 ne suka kammala karatunsu a wannan shekarar, inda suka yi fice a fannoni daban-daban na kimiyyar zamantakewa da ta ɗabi'a.
A yayin bikin da aka gudanar a Istanbul ranar Laraba, ɗalibai daga Afirka da sauran nahiyoyi sun karbi takardun shaidar karatunsu daga jami’o’i 38 daban-daban a Türkiye.
Tasirin Maarif na ƙara girma
Bayan sun fara karatu a Makarantun Maarif a kasashe kamar Somalia, Tunisia, Sudan, Guinea, Nijar, Mali, Habasha, Morocco, Burundi, da Mauritania, yanzu daliban Afirka suna shirin komawa kasashensu don zama jakadun alheri.
Wannan na zuwa ne yayin da dangantaka tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka ke kara karfi.
Da yake jawabi a bikin, Shugaban Asusun Maarif na Turkiyya, Mahmut Mustafa Özdil, ya bayyana cewa asusun, wanda aka kafa shekaru tara da suka gabata, yanzu yana aiki a kasashe 55 a nahiyoyi shida, inda ya kai ga dalibai sama da 70,000 a duniya.
“Makarantun Maarif suna koyar da mutane su kasance masu kame kansu a al’adunsu yayin da suke mu’amala da duniya baki daya. Tsarinmu ba ya tilasta wa kowa, yana mutunta dabi’un gida, kuma yana girmama ka’idojin duniya.
“Ba wai kawai kun zama kwararrun dalibai ba ne, har ma kun zama gada mai aminci na dabi’u tsakanin kasashensu da Turkiyya,” in ji Özdil, yana mai jaddada tsarin ilimin na musamman na asusun.
‘Murya ga marasa murya’
Da yake wakiltar wadanda suka kammala karatun, Hamza Yimaj Hussien daga Habasha ya jaddada cewa Maarif ba kawai tana kula da nasarar karatu ba, har ma tana koyar da dabi’u masu kyau.
“Abin da ke faruwa a Gaza yana karya zuciyarmu. Maarif ta koya mana mu zama masu tausayi da adalci baya ga kasancewa masu nasara. Dole ne mu zama murya ga marasa murya,” in ji shi.
A wani lokaci mai ma’ana a yayin bikin, Muhammed Ahmed Alasow — wanda ya kammala karatu daga Makarantar Maarif ta Mogadishu da Jami’ar Istanbul Medipol — ya mika tutar Maarif ga Mahamat Saleh Khamis, dalibi daga Makarantar Maarif ta N’Djamena a Chadi kuma dalibi a Jami’ar Ankara Hacı Bayram Veli.
Bikin ya kare da harba jiragen takarda masu zane na kankana — alamar juriya ta Falasdinu — da daukar hotuna.
Daga cikin mahalarta akwai Mataimakin Gwamnan Istanbul M. Asım Alkan, mambobin kwamitin amintattu na asusun, shugabanni, iyalai, da ma’aikata.