Matsalolin tsaro da kariya da Turai ke fuskanta a halin yanzu suna da nasaba da "gurguwar dabararta” a kan yadda take kallon Turkiyya, in ji wani babban dan majalisar Turkiyya, yana mai gargadin cewa wannan kuskuren na iya cutar da Turai kanta.
Fuat Oktay, shugaban kwamitin harkokin waje na Majalisar Dokokin Turkiyya kuma dan majalisa daga jam’iyya mai mulki ta AK Party, ya bayyana cewa rashin kayan aikin soja da kuma damuwar da ake fama da ita a Turai suna da nasaba kai tsaye da wannan kuskuren na dabarun tsaro.
“Rashin kayan aikin soja da yanayin damuwa da ake ciki a Turai suna da nasaba da wannan makanta ta dabarun tsaro,” in ji Oktay a hirarsa da gidan talabijin na Turkiyya, TRT Haber, a ranar Litinin, yayin ziyararsa a ofishin TRT World da ke London a gefen taron Concordia Europe Summit, wani babban taron masu tsara manufofi.
Ya jaddada cewa wannan kuskuren bai ɓuya daga idanun Ankara ba, yana mai nuna yadda ake rage darajar rawar da Turkiyya ke takawa wajen tsaron Turai duk da muhimmancinta.
Oktay ya bayyana cewa barazanar tsaro a yau ba ta tsaya kawai ga hare-haren soja da aka saba gani ba. “Barazanar ba ta fito daga hare-haren soja kawai ba, har ma da wasu fannoni kamar ta’addanci da hare-haren intanet da kuma kwararar ‘yan gudun hijira,” in ji shi.
A cewarsa, Turai dole ta daina ganin kanta a matsayin cibiyar duniya idan tana son magance matsalolinta na yanzu. “Mun so isar da sakon cewa ya kamata Turai ta daina ganin kanta a matsayin cibiyar duniya,” in ji shi.
“Mun bayyana cewa za ta iya fita daga wannan makanta ta dabarun tsaro idan ta ga kanta a matsayin wani bangare na duniya, ba cibiyar duniya ba... kuma daga wannan hangen nesa, Turkiyya tana cikin matsayi mafi aminci dangane da tsaron Turai.”
Ya jaddada cewa al’ummar Turkiyya mai bambancin addinai da ra’ayoyi na iya ƙara wa Turai karfi idan aka fi hada kai da ita cikin tsarin tsaron Turai da ke ci gaba da sauyawa.
Babbar mai taka rawa
Taron ya zo ne a daidai lokacin da ake muhawara mai zafi a Turai kan gina sabon tsarin kariya.
Yayin da Amurka ke sauya matsayinta karkashin shugabancin Donald Trump, EU tana tunanin kafa wani ƙawancen kariya ta hadin gwiwa da ba ta dogara sosai kan tallafin soja na Washington ba.
Furucin Trump cewa hakkin Turai ne, ba Amurka ba, ta tabbatar da tsaron Ukraine ya ƙara tsananta wannan muhawarar.
Don magance wadannan damuwar, EU ta kafa wani dandali mai suna “kasashen da ke da ra’ayi iri daya” don daidaita manufofin tsaro tare da mambobin NATO, ciki har da Turkiyya—wadda ke matsayin ƙawa NATO kuma ƙasa mai neman shiga EU.
Duk da sabanin da aka samu kwanan nan, Turkiyya ta ci gaba da kasancewa babbar mai taka rawa a tsarin tsaron Turai. Oktay ya nuna ci gaban da kasar ta samu a masana’antar tsaro da kuma ƙarfinta na tura sojoji zuwa fagen fama.
“Turkiyya, wacce ita ce kasa ta biyu mafi karfi a NATO, ita ce kasa wadda ta fi zama cikin shiri a Turai dangane da masana’antar tsaro da karfin da za ta iya tura sojojinta fagen fama,” in ji shi.
Dangantakar tsaro tsakanin Turkiyya da abokan NATO ta samu matsala saboda takunkumin da Amurka ta kakaba bayan Turkiyya ta sayi tsarin makamai na Rasha S-400.
Wadannan takunkumin sun sa Turkiyya ta fita daga shirin jiragen yaƙi na F-35 da Amurka ke jagoranta.
Duk da haka, Oktay ya jaddada cewa hadin kai da Turkiyya yana da matukar muhimmanci.
“Mun yi kokarin bayyana cewa yin aiki tare da Turkiyya a sabon tsarin tsaro da fita daga wannan makanta ta dabarun tsaro zai kasance cikin maslahar Turai kanta. Za mu ci gaba da bayyana wannan a kowane lokaci.”