SIYASA
8 minti karatu
Kuskuren Amurka na korar Jakadan Afirka ta Kudu Ebrahim Rasool
Kowacce kasa na iya ayyana jakadan wata kasar a matsayin mutumin da ba ta bukata kamar yadda Yarjejeniyar Vienna ya tanada. Amma ba don karamin dalili irin haka ba.
Kuskuren Amurka na korar Jakadan Afirka ta Kudu Ebrahim Rasool
The strained relations between Washington and Pretoria ultimately boils down to South Africa taking Israel to the International Court of Justice. / Reuters
17 Maris 2025

Daga Na'eem Jeenah

Mun san juna da Ambasada Ebrahim Rasool tsawon lokaci. A farkon 1980, dukkan mu mun shiga gwagwarmayar kalubalantar mulkin farar fata tsiraru.

A ranar Juma’a na karbi bakuncin taron ƙara wa juna sani ta intanet a Cibiyar Bincike da Nazari ta Mapungubwe (MISTRA) inda muka duba me manufofin Amurka ke nufi a shekaru hudu masu zuwa ga nahiyar Afirka, musamman ma ga Afirka ta Kudu.

Manufar da muka tattauna a kai ita ce sabuwar gwmanatin Amurka da tasirinta kan Afirka, yankin Kudancin Afirka da ma kasar Afirka ta Kudu.

Jakada Rasool ya zama zabi mai kyau na wanda aka gayyata don yin jawabi a taron na yanar gizo.

Ya zauna a Amurka na kusan watanni biyu, kuma kafin hakan, ya zauna a kasar na shekaru hudu a matsayin jakadanmu a Wahsington.

Rasool ya san siyasar Amurka sosai, kuma yadda yake dan kasar Afirka ta Kudu, ya fahimci abubuwan da ake baiwa fifiko a alakar Afirka ta Kudu da Amurka.

An kuma gayyaci wasu masu jawabi su hudu don duba wannan batu a taron karawa juna sanin na tsawon awanni hudu.

Ikirarin ƙarya da Trump ya yi kan Afirka ta Kudu

A bayanin bude taron, Jakada Rasool ya bayyana irin muhimmancin alakar Afirka ta Kudu da Amurka.

Amurka na daya daga manyan abokanan kasuwancin Afirka ta Kudu.

Yana da ra’ayin cewa duk da umarnin da Trump ya bayar na kalubalantar Afirka ta Kudu, to kar kasar ta dauki matakin nuna adawa ga Amurkan.

Duba ga kasuwancinmu, ya yi karin haske da cewa a yayin da kashi 80 na kayan da China ke saya daga Afirka ta Kudu suka kasance sinadarai ne da ba a sarrafa ba, Amurka na sayen kashi 70 na kayayyakin da aka samar a Afirka ta Kudu.

A wajen tambaya da amsa, an tambaye shi game da me ra’ayins akan me ya sa gwmanatin Trump ta dauki wannan babban mataki kan Afirka ta Kudu.

Umarnin Zartarwar da Trump ya bayar ya ambaci abubuwa biyu.

Dayan shi ne kamar yadda Trump ya fada daga baya, “Akwai munanan abubuwa da ake yi a yanzu haka a Afirka ta Kudu”.

Sai dai kuma, abin da umarnin ke bayyanawa shi ne akwai wasu mutane da ake nuna wa wariya, kuma ya yi bayani a kan haka tare da tabo wata doka, wadda ya yi karyar cewa ta tanadi gwamnati ta kwace gonaki da sauran su.

Karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra’ila

Yana nufin Dokar Gwamnati ta Karbi Kadarorin Jama’a ta yi amfani da su, wadda Shugaban Kasa Cyril Ramaphosa ya sanya wa hannu a watan Janairun wannan shekarar amma har yanzu ba a fara aiki da ita ba.

Saboda haka, babu wata gona ko fili na wani da aka kwace. Wannan ne dalilinsa na farko na daukar matakin.

Dalili na biyu shi ne karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra’ila Kotun Kasa da Kasa, ICJ, inda Pretoria ta zargi Tel Aviv da aikata kisan kiyashi a Gaza,

Da yake amsa wannan tambaya, Jakada Rasool ya yi bayani ga ‘yan Afirka ta Kudu da ke kallo da saurarensa yadda sabuwar gwamnatin Amurka ke aiki.

Ya yi tsokacin cewa nan da wasu ‘yan shekaru masu zuwa, yanayin jama’ar Amurka zau sauya inda kashi 48 na MAurkawa ne akwai za su kasnace farar fata, kuma gwamnatin Trump ta bayyana fararen hula kawai za ta dinga karewa.

Ya kara da cewa a yayin da wannan batu ne na cikin gida, gwamnatin ta Trump na bayyana wannan hala a duniya baki daya.

Misali, Mataimakin Shugaban Kasa JD Vance ya dinga ambatar darajar masu nuna wariyar launin fata, yana yabon jam’iyyar AfD mai tsaurin ra’ayi da ke kyamar ‘yan gudun hijirar Jamus da dan siyasa mai ra’ayin rikau na Birtaniya Nigel Farage.

Gwamnatin Trump na da irin wannan halayya ga fararen fatar Afirka ta Kudu, sia ka ce gwamnatin ta Trump na kare dukkan fararen fata na duniya ne.

Martanin da Amurka ta mayar

Jakadan ya yi kokarin fayyace cewar abinda muke shaida wa kamar wani salon nuna fifikon farar fata ne.

Wannan ne dalilin da ya sanya Breibart yi azarbabi a shafinsu na yanar gizo na masu tsaurin ra’ayun a Amurka.

Joel Pollak, dan Amurka haifaffen Afirka ta Kudu kuma mai ra’ayin rikau da ke sharhin siyasa, kuma yake neman zama jakadan Amurka a Afirka ta Kudu, shi ne ya rubuta makalar da aka fitar a shafin na Breibart

Pollak, ya yi amfani da wannan batu na sauyawar yanayin jama’ar Amurka da yadda gwamnatin Trump ke son kare muradun fararen fata kawai.

Wannan makala ce Sakataren Harkokin Waje Marco Rubio ya karanta tare da amfani da ita wajen aike wa da sako ta shafin X tare da bayyana jakadan Afirka ta Kudu Ebrahim rasool a matsayin wanda ba a bukatar gani a Amurka.

Afirka ta Kudu ba ta adawa da Amurka

Abu ne da ba a saba gani ba ga sha’anin diflomasiyya, saboda wannan abu, a ce wai jakada ya zagi shugaban Amurka ko kasar.

Mutum zai yi tsammanin cewa matakin farko da za a dauka shi ne shata layi ko kokarin ministocin harkokin wajen kasashen biyu su tattauna kan abinda jakadan ya aikata.

Maimakon haka, sai ga shi sun wuce gona da iri tare da ayyana Jakada Rasool a matsayin wanda ba a son gani a Amurka, matakin da akan dauka a kan jami;in diflomasiyya da ya yi leken asiri ko satar bayanai.

Asali dai, duk mun yi shiru cikin mamaki da muka samu labarin hakan, awanni kadan bayan wannan taro ta yanar gizo, cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya dauki wannan mataki kan jakadanmu. Abin na da ban mamaki.

Jakadan ya yi gaskiya kuma da yin jawabi karara, kuma ba mu ga wani abu a tattaunawar tasa da zai sa a dauki wannan matakin a kansa ba.

Jakada Rasool ya yi aiki a Amurka a baya.

Ba na tunanin wani, da ya yi mu’amala da shi a wannan mataki, ko Afirka ta Kudu ko Amurka babu wanda zai masa kallon ba ya kaunar Amurka.

Sabanin haka, ana sukarsa saboda yin kalami masu dadi ga Amurka bayan kalamansa a nan, musamman wajen kira ga ‘yan Afirka ta Kudu da su kiyaye daga mayar da martani marar kyau ga umarnin na Trump. Ba shi da wani hali na adawa ga Amurka.

An aika shi kasra aiki ne saboda zai iya habaka alakar kasashen biyu a wannan lokaci na tsaka mai wuya, kuma a karshe, ya bayyana Afirka ta Kudu da shi kansa a matsayin kawayen Amurka.

Da a ce shugaban kasarmu ya san ba ya kaunar Amurka, da bai tura shi jakadanci a Washington ba.

Babban dai dalilin wannan rikici shi ne Afirka ta Kudu ta kai karar Isra’ila Kotun Kasa da Kasa.

A yanzu akwai batutuwa biyu game da hakan:

Na farko dai shi ne kudirin gwamnatin Trump na kare Isra’ila ta kowane hali.

Ba ja da baya kan karar kisan kiyashi a Kotun Kasa da Kasa

Karar da Afirka ta kai Isra’ila Kotun Kasa da Kasa ne ya sanya ta shiga takun saka da Amurka.

Abu na biyu shi ne yadda gwamnatin Trump ke bayyana ba ta girmama wata hukuma ta kasa da kasa ko dokokin kasa da kasa. A wani kaulin, ta hanyar saln da take bi, dokar karan tsaye ce za ta dinga juya al’amuran duniya a yau.

Game da Kotun Kasa da Kasa kuma, Afirka ta Kudu ta bayyana karara cewa ta dauki wannan mataki ne saboda akida - aiki da dokokin kasa da kasa da kuma cewa a matsayinmu na al’ummun duniya babu yadda za a yi a a ince da take dokokin kasa da kasa ana kallon Isra’ila na ta\annati a Gaza.

Afirka ta Kudu ba za ta ja da baya ba game da wannan. Gwamnatin Afirka ta Kudu kuma, ta yi amanna da aiki da kundin tsarin mulkinta sannan ta habaka yin adalci da kare hakkokin dan adam a duniya baki daya, wannan ne abinda muke yi.

Dadin dadawa, yadda Afirka ta Kudu ta samu goyon baya daga kasashen duniya musamman na Kudancin Duniya, ba ma za ta iya janyewa daga karar ba, idan aka kalli matsayin alakar kasa da kasa.

Afirka ta Kudu ba ta fito don yin gaba da Amurka ba, tana son warware matsalolin cikin diflomasiyya, kamar yadda shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana a jawabinsa na kasa da ya yi a lokacin da ya ce ba za a iya zaluntar kasar ba, kuma za mu yi hulda da kasashen duniya cikin mutunci da daraja.

Marubuci, Na’eem Jeenah babban mai bincike ne a Cibiyar Mapungubwe MISTRA.

Togaciya: Ra'ayin da marubucin ya bayyana ba lallai ba ne ya zo daidai da ra'ayi,hange da manufofin editan TRT Afrika.


MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us