SIYASA
2 minti karatu
Turkiyya ta ce ana ci gaba da sanya idanu sosai kan ‘yan ƙasar da ke cikin jirgin ruwan Madleen
Majiyoyin diflomasiyya sun bayyana cewa ana sanya idanu sosai kan ‘yan Turkiyya da ke cikin jirgin da Isra’ila ta kama a lokacin da suke kan hanyar kai kayan agaji zuwa Gaza, in ji majiyoyi daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.
Turkiyya ta ce ana ci gaba da sanya idanu sosai kan ‘yan ƙasar da ke cikin jirgin ruwan Madleen
Wadanda aka kama sun sako daga kan jirgin ruwan tun ranar Litinin, kuma jami'an Ofishin Jakadancin Turkiyya a Tel Aviv sun ziyarce su. / Public domain
10 Yuni 2025

‘Yan Turkiyya da ke cikin Madleen, jirgin ruwan da dakarun Isra’ila suka kama a yayin koakrn kai kayan agaji zuwa Gaza, na karkashin sanya idanu sosai, in ji majiyoyi a Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar.

Wadanda aka kama ɗin sun sauka daga kan jirgin ruwan tun ranar Litinin, kuma jami'an Ofishin Jakadancin Turkiyya a Tel Aviv sun ziyarce su.

An bayar da duk wani taimakon diflomasiyya ga ‘yan kasar Turkiyya, kuma an sanar da iyalansu halin da ake ciki, in ji majiyoyin a ranar Talata.

A matsayin wani bangare na ayyukan ƙungiyar farar hula ta “Freedom Flotilla Coalition” da ke da manufar bude hanyar da aka toshe don zuwa Gaza tare da kai kayan agaji ga yankin, jirgin ruwan mai tsayin kamu 59 ya tashi a ranar 1 ga Yuni daga tasar jiragen ruwa ta San Giovanni Li Cuti da ke Catania, Italiya, inda ya nufi Gaza.

Masu fafutuka da ke cikin jirgin ruwan sun bayyana cewa za su zama masu zaman lafiya, kuma ba za su nuna tirjiya ba idan sojoji Isra’ila suka yi musu kutse.

A ranar Litinin ne Isra’ila ta afka wa jirgin ruwan na Madlees, wanda ke kan aniyar buɗe hanyoyin kai kayan agaji Gaza da aka toshe.

A cikin jirgin ruwan akwai mambar Majalisar Dokokin Turai Rima Hassa ‘yar ƙasar Faransa, da ‘yar Jamus Yasemin Acar, da Huseyin Suayb Ordu daga Turkiyya, da Thiago Avila daga Brazil, da Sergio Taribio daga Sifaniya, da Maco van Rennes daga Holland, akwai kuma Baptiste Andre, Reva Viard, Pascal Maurieras, da Yanis Mhamdi daga Faransa, sai mai fafutukar kare yanayi ‘yan Sweden Greta Thunberg, da ɗan jarida Omar Faiad.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us