SIYASA
7 minti karatu
Larabawa Musulmai da Farar Fata Kiristoci? Wa ake kira ɗan ta’adda waye ba a kira da hakan?
Bayan wani dan Birtaniya farar fata ya take jama’a a wajen taron nasarar Liverpool, mahukunta sun yi gaggawar musanta ta’addanci, duk da jikkata sama da mutane 100. To me ya sa ake bayar da wata ma’ana ta daban idan baki ko Musulmi ne ya aikata hakan
Larabawa Musulmai da Farar Fata Kiristoci? Wa ake kira ɗan ta’adda waye ba a kira da hakan?
A watan da ya gabata an jikkata mutane 109 a wani hari na ganganci da aka kai kan jama'a da ke murnar nasarar Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool. / Reuters
11 Yuni 2025

Daga Sunniya Ahmad Pirzada

Bayan hari d amota da aka kai kan masu murnar nasarar lashe gasar Premir ta Ingila da kungiyar Liverpool ta yi - lamarin da ya janyo jikkata mutane 109, wanda mafi kankantarsu dan shekara tara da mafi tsufa dan shekaru 78 - ‘yan sanda sun yi abinda ba a saba gani ba.

Cikin awanni, suka bayyana sunan wanda ya aikata laifin, Paul Doyle, mai nshekaru 53 kuma farar fata dan kasar Birtaniya daga yankin West Derby.

Daga cikin Musulmai ‘yan Birtaniya, sun samu sauki a zukatansu. Saboda gaskiyar ita ce: da a ce wanda ya kai harin Musulmi ne, ko kuma ba farar fata ba ne, to da kanun labarai ya sha bam-ban da wannan, kuma da tuni an fara tsangwamar al’umma.

A baya ma mun shaida hakan. A watan Agustan 2024, rahotannin karya da ke ikirarin wanda ake zargi da caka wa wani wuka a Southport dan gudun hijira ne ko kuma Musulmi sun janyo zanga-zanga a fadin Birtaniya.

An kai hari kan wuraren kasuwancin Musulmai. An kai hari gidajen otel da Musulmai ke kwana a ciki.

Duk hakan ya faru ne saboda bayanan karya da aka fitar da mahukunta suka kara kalubalanta a kan lokaci. Wanda ya kai harin, an gano ba dan gudun hijira ba ne kuma ba Musulmi ba ne. Amma an riga an yi barnar.

Bayanan farko, musamman wadanda suka hada da kabilarsa, watakila na da manufar dakatar da yawaitar jita-jita a shafukan yanar gizo, wanda cikin sauri ka iya zama bayanan karya masu hatsari. Har yanzu, ‘yan sanda sun bayyana wani abu guda karara; duk da shaidun gani da ido na kawo bayanai, amma ba a yi wa batun kallon na ta’addanci ba.

Doyle da laifuka da dama, ciki har da mummunan tuki da niyyar jikkata gangar jikin mutane. Amma fa ba wai ta’addanci ba.

Wannan ne dalilin da ya sanya yake da muhimmanci aka yi gaggawar bayyana sunan Paul Doyle dan Birtaniya farar fata - ke da muhimmanci. Karara, ‘yan sanda na daukar darasi da kura-kuransu na baya.

Watakila sun fara gano cewa shiru da jan kafa na jayo abubuwa masu hatsari. Kuma dai, abin tambayar da ba ya gushewa shi ne: me ya sa mutum kamar Doyle, wand aaka zarga da kutsa kai cikin dandazon jama’a da gangan, ba za a bayyana shi a matsayin dan ta’adda ba?

Ta’addanci ta BIrtaniya ta 2000 ta fitar da bayanai karara. Ta’addanci ya hada da amfani da barazana ko rikici mummuna ga mutane, lalata dukiya, ko wani abu mai hatsari ga rayuwa ko zaman lafiyar jama’a, wanda aka yi don daukar hankalin gwamnati, barazana ga jama’a, ko don bayyana siyasa, addini, launi ko akidar da mutum ke bi.

Amma duk da haka bayan wucewar lokuta, ana nuna zabi da wariya wajen aiwatar da wannan ta’arifi.

Mun ga lamarin Salih Khater. A watan Agustan 2018, ya tuka mota tare da kutsa kai kan wasu masu tafiya a kafa a wajen Majalisar Dokokin Landan da ke Westminster.

Nan da nan aka kama shi, aka tsare shi karkashin Dokar Ta’addanci, inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Ba shi da alaka da wata kungiyar ta’addanci. Babban Masallacin Birmingham ya tabbatar da cewa ba a ma san shi da yin Ibada a wajen ba kuma ba a ga alamun tsaurin ra’ayi a tare da shi ba.

Amma saboda kalarsa ba fara ba ce, mai neman mafaka ne daga SUdan da ya zama dan kasar Birtaniya. Dalilin kenan.

Abinda Khater ya aikata iri daya ne da ta’annatin da Doyle ya yi. Amma a yayin da aka bayyana Khater a matsayin dan ta’adda, Doyle kuma ana yi masa wani mutum da ya aikata mummunan laifi, da ba shi da alaka da wata akida ko zamantakewar al’umma.

To me ke kawo hakan?

Siyasar ‘asalin mutane’

Ba zai yiwu a yi biris da yadda ake bayyana waye wanda ya aikata laifin - launin fatarsa, addini, matsayinsa, da kasar da ya fito - ba iya labaran da kafafan yada labarai ke fitar suka yi wa tasiri ba, har ma da sigar da aka bi wajen bayyana laifin.

Siffar dan kasar Birtaniya farar fata a gatan zamantakewa da siyasa kawai yake samu ba, har ma da wata kariya wajen bayar da labarai a kan sa.

Da zarar an furta wadannan kalmomi, sai kafafen yada labarai, jama’a, da ‘yan sanda ma sai su fara tausasa harshe: sharrin amfani da ƙwaya, matsalar kwakwalwa (Doyle tsohon ma’aikacin jirgin ruwa ne), batutuwan kebantuwa.

Amma idan da gangan aka jikkata mutane 109, da suka hada da yara kanana, wannan ba ta’addanci ba ne? Shin ba a firgita da illata wadanda ta’annatin ya rutsa da su ba?

Maganar gaskiya ita ce, ta’addanci ya zama kalma da ake alakanta ta da launin fata, inda ake yawan bayyana ta’addanci a matsayin na Musulunci.

Ana aiki da kalmar ne idan wanda ya kai hari bakar fata, Musulmi, wanda aka haifa a kasar waje ko wanda ya hada dukkan siffofin uku ne kawai.

Amma kuma munanan ayyukan da farar fata ke aikatawa, ba sa hawa kan wannan sikeli ko da kuwa ta’annatin nasu ya dace da tanadin doka ta yi.

Wannan fuska biyu ba jirkita fahimtar da muka yi wa ta’addanci ai yi kawai ba, har ma da jefa hakan cikin hatsari.

Ta hanyar bayyana ta’addanci a matsayin aikin da Musulmai ne kadai suke aikata shi, zai zama ba a ganin yadda barazanar rikicin masu tsaurin ra’ayi ke kara girmama.

Abin da ake biyo baya ma ya fi muni. Wadanda suke daga gefe - Musulmai, ‘yan gudun hijira, al’ummun d aake nuna wa wariyar launin fata - na fuskantar tsana da twangwama, ana tirsasa su su dauki nauyin laifin da ba su aikata ba. Su kuma farar fata masu aikata ta’annatin fa?

Suna zaman su a matsayin daidaikun mutane, ana bayyana laifukansu a matsayin rashi nansarar kawunansu, ba wai wata barazana ga kowa ba.

Rashin daidaito a kalaman d aake amfani da su da mayar d amartani ba bata rai kawai ke yi b, na da hatsari ma.

Na jirkita fahimtar mutane kan mene ne ta’addanci, kuma mafi muhimmanci ma shi ne waye zai iya zama dan ta’adda. Ana bayar da damar shaidantar da wata al’uma baki daya, yayin da ake kuma kare wata.

Harshe na da muhimmanci a nan. Kalmomin da muke amfani da su na tasiri kan tsarin adalci da shari’a, na tasiri kan tunanin jama’a, da jan gorar aiwatar da manufofin siyasa.

Yadda ake ci gaba da kin kiran masu aikata laifuka farar fata da ‘yan ta’adda na aike wa da sako mummuna: wasu ‘yan rayuka ne ke da daraja. Wasu ayyuka ne suke bukatar doka ta yi aiki a kan su yadda ya dace.

Ba ma son a samu karin mutanen da za a kira ‘yan ta’adda. Wannan kalma na dauke da mummunan sakamako. Amma muna bukatar adalci da daidaito ta yadda kalmar ba za ta zama mai kan wasu da ake zalunta ko nuna wa wariya ba. Kar kalmar ta zama makamin hantara da cusgunawa.

Idan har ta’addanci na nufin wani abu, to dole ne a dinga aiki da kalmar a kan duk wanda ya aikata ta’addanci, ba wai a kan wasu wararru ba.

Idan ba haka ba, to ba fa adalci muke yi ba, bambanci da gaba ne muke kitsawa a doron shari’a, To bari mu tambayi kawunanmu: Shin ta’addanci ya shafi abinda ka aikata ne ko kuma ya shafi waye kai ne?

Matukar ba mu samu amsar wannan ba, to fa tsarin shari’a zai ci gaba da kasancewa mai hatsari saboda na nuna wariya da bambanci.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us