A cikin hotuna: Yunwa a Gaza
A cikin hotuna: Yunwa a Gaza
An fara aiwatar da wani sabon shirin agajin da Amurka ke mara wa baya yayin da yunwa ke ƙara ta'azzara a Gaza - inda aka ba da rahoton mutuwar fiye da mutum 326 sakamakon yunwa a cikin watanni uku, sannan fiye da miliyan ɗaya ke barazanar faɗawa fari
26 Mayu 2025

Yayin da sabon shirin raba tallafi da Amurka ke goyon baya ya fara a Gaza ranar Litinin, halin jinƙai na ci gaba da taɓarɓarewa a yayin da Isra'ila ta sake kai hare-haren soja.

Ga yadda gaskiyar mummunan yanayin da Falasdinawa ke fuskanta a Birnin Gaza yake — an kore su daga gidajensu, suna fama da yunwa, kuma an bar su cikin halin ƙunci — abin kamar yadda za a gani a hotunan nan.

Daraja ta zube

Yunwa ta zama ruwan dare a Gaza, inda mazauna yankin ke bin layi na tsawon sa'o'i—sau da yawa ba tare da samun komai ba— duk a ƙoƙoarinsu na samun buhun fulawa ɗaya ko burodi.

Bisa ga rahoton Majalisar Dinkin Duniya, fiye da mutum miliyan 1.1—rabin yawan jama'ar Gaza—na fuskantar matsanancin rashin abinci, kuma ana gab da faɗawa yunwa idan ba a ƙara tallafi cikin gaggawa ba.

Takunkumin hana shigar da abinci da ruwa da Isra'ila ta ƙaƙaba tun bayan ranar 7 ga Oktoba na ƙara tsananta inda ya takaita shigar da abinci, ruwa, da magunguna, wanda ya jefa yankin cikin halin jinƙai mara misaltuwa.

Lamarin ya ƙara taɓarɓarewa tun ranar 2 ga Maris, 2025, lokacin da sabon kulle ya kawo kusan cikakken rufe iyakokin shiga da dakatar da yawancin tallafi.

Zamani mai rauni

A arewacin Gaza, asibitoci sun cika da yara masu fama da matsanancin rashin abinci, da dama daga cikinsu na fama da rashin kuzari da rashin ruwa a jiki.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Harkokin JinƘai (OCHA) ya bayyana cewa yara da dama sun riga sun mutu sakamakon matsalolin da suka shafi yunwa.

Sabon kulle da Isra'ila ta kafa tun ranar 2 ga Maris ya haifar da mutuwar mutum 326 da kuma ɓarin ciki 300, kamar yadda Ofishin Watsa Labarai na Gaza ya sanar a makon da ya gabata.

Har yanzu ba a samu damar kai tallafi zuwa arewacin yankin ba, kuma kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa yankin na iya kasancewa cikin yunwa mai kisa ba tare da an lura ba.

An dauke su kamar dabbobi

Yayin da kasuwanni suka zama kufai da kuma hana shigar da isar da abinci, iyalai da dama sun koma tafasa ciyawa, ganye, da abincin dabbobi don tsira.

"Ina jin kunya sosai da ba zan iya ciyar da 'ya'yana ba," in ji Mevat Hijazi, mahaifiyar yara tara, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters daga tantinsu da aka kafa a cikin baraguzan Birnin Gaza.

"Nakan fashe da kuka duk dare lokacin da jaririyata ke kuka kuma cikinta na ciwo saboda yunwa."

Ana kallon ruwa amma ba damar sha

Motoci cike da kayan agaji na jinƙai suna ci gaba da jiran a bar su su wauce a iyakar Rafah ta Masar, inda ake jinkirta musu samun damar shiga ko hana su saboda shingayen binciken tsaro na Isra'ila da takunkumai.

Shirin Abinci na Duniya ya ce ƙasa da kashi daya cikin hudu na abincin da ake bukata ne ke shiga Gaza.

A wannan makon, kadan ne daga cikin motocin tallafi suka shiga, wanda bai kai matsakaicin adadin da ake bukata kowace rana don kauce wa yunwa ba.

Bala’in yunwa

Yunwa babbar bala’i ce ga ɗan’adam da a yanzu ba gabatowa kawai take ba — ta riga ta zama gaskiya.

Wani yaro dan shekara 10 dan Falasdinu, Yazan al-Kafarna, wanda aka haifa da cutar galahanga wato cerebral palsy, ya rasu a watan Maris 2024 saboda abin da likitansa ya ce matsanancin rashin kuzari da rashin abinci.

Wannan hoton ban tausayi na Yazan mai nuna ba komai a jikinsa sai ƙashi da fata, yana kwance a asibiti a Rafah ranar 3 ga Maris, 2024, ya yadu sosai a kafafen sada zumunta kuma ya zama gargadi mai karfi game da matsanancin yanayin rashin abinci a Gaza.

Bisa ga rahoton Save the Children, adadin mutuwar yara daga yunwa na ƙaruwa, sannan ɗaruruwan yara na cikin hadari.

Wadannan mace-mace za a iya kauce musu—tun da ba haka nan suka faru ba, da gangan ɗan’adam ya yi sanadinsu.

Dogon jira

Ko da inda tallafi ya isa, kayan ba sa isa su cika bukatun mutane. Mutane na layi na tsawon sa'o'i, sau da yawa suna kwana a kusa da wuraren rabon tallafi don ƙara damar samun nasu.

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta gargadi cewa kayan ajiyarta na raguwa, yayin da manyan kantuna suka fuskanci hare-hare kuma hanyoyin shiga sun kasance masu hadari.

"Muna zabar wanda zai ci," wani ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya ya fada cikin baƙin ciki, "saboda ba za mu iya ciyar da kowa ba."

Haka ya isa!

Yayin da fushin al’ummar duniya ke ƙaruwa, kungiyoyin jinƙai na kira da a gaggauta tsagaita wuta da kuma samun damar kai tallafi ba tare da wani shinge ba.

"Ba batun dabaru ba ne. Batun niyya ne," in ji Martin Griffiths, Kwamishinan Agajin Gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya.

Ba tare da wani matakin diflomasiyya cikin gaggawa ba, kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa dubban mutane za su mutu daga yunwa, ko da an dakatar yaƙin a yanzu.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us