24 Afrilu 2025
Da yake hira da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Tinubu ranar Laraba, Mallam Nuhu Ribadu ya ce shugaban ƙasar ya bai wa jami'an tsaron Nijeriya umarnin ƙara ƙaimi wurin shawo kan rashin tsaro kuma za su bi umarninsa ba tare da ɓata lokaci ba.