NIJERIYA
1 minti karatu
A asibiti ɗaya na yi jinya da Buhari, amma ni an sallame ni – Abdulsalami Abubakar
Tsohon Shugaban Nijeriya Abdulsalami Abubakar ya aika saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, inda ya ce a asibiti ɗaya suka yi jinya a birnin Landan.
A asibiti ɗaya na yi jinya da Buhari, amma ni an sallame ni – Abdulsalami Abubakar
Tun bayan rasuwar Shugaba Buhari, shugabannin duniya da dama da tsofaffin shugabanni ke aika saƙon ta’aziyya. / Others
14 Yuli 2025

Tsohon Shugaban Nijeriya Abdulsalami Abubakar –der  ya bayyana cewa a asibiti ɗaya suka yi jinya da Buhari kafin rasuwarsa, amma shi an sallame shi.

Tsohon shugaban na Nijeriya ya bayyana haka ne a yayin da yake ta’aziyya da nuna alhininsa game da rasuwar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, ya bayyana cewa ya san Buhari tun a shekarar 1962 kuma tare suka yi yaƙin basasa.

Ya bayyana Buhari a matsayin mutumin kirki kuma mai gaskiya sanan ya ce ya yi iyakar bakin ƙoƙarinsa domin ganin ya ɗora Nijeriya a bisa saiti.

Abdulsalami ya kuma bayyana cewa sakamakon rasuwar Buhari, salon siyasar Nijeriya za ta sauya baki ɗaya.

Tun bayan rasuwar Shugaba Buhari, shugabannin duniya da dama da tsofaffin shugabanni ke aika saƙon ta’aziyya.

Ana sa ran gudanar da jana’izar Buhari a ranar Talata, 15 ga Yulin 2025 a mahaifarsa Daura.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us