Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce jerin matsaloli da hare-haren Isra’ila suka haifar za su iya lahani ga yankin Turai game da gudun hijira da kuma yiwuwar yoyon nukiliya.
A tattaunawar da suka yi ta waya da Shugaban Jamus Friedrich Merz, Erdogan ya ce kamata yayi a warware rashin jituwar nukiliya da Iran ta hanyar tattaunawa kuma ya yi gargaɗin cewa hare-haren Isra’ila sun ƙara zama barazana ga tsaron yankin, in ji hukumar sadarwa ta Turkiyya.
"Shugaban ƙasarmu ya kuma yi gargaɗin cewa tashin hankalin da hare-haren Isra’ila suka haddasa za su iya mummunan tasiri a yankin da kuma Turai, musamman game da yiwuwar gudun hijira da kuma abin da ke iya biyo bayan [matsalar] nukiliya," kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na X.
Shugaba Erdogan ya ce matsalar, wadda ta fara da harin Isra’ila a kan Iran, ya zama barazana ga tsaron yanki.
Shugabannin biyu sun kuma tattauna dangantakar da ke tsakanin ƙasashensu da kuma batutuwa na yanki, in ji hukumar.