Birtaniya da wasu ƙawayenta na ƙasa da ƙasa sun ƙaƙaba takunkumai ga wasu ministocin Isra’ila biyu masu tsattsuaran ra’ayi, Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich, saboda abubuwan da suka yi a yaƙin Gaza, in ji rahoton jaridar The Times.
Landan ta bi sauwn Canada, da Australia, da New Zealand da wasu ƙasashen wajen sanya takunkumai kan kadarorin Ministan Tsaron Ƙasa na Isra’ila Ben-Gvir, ɗan kama-guri-zauna a Yammacin Kogin Jordan, da Ministan Kudi Smontrich, in ji jaridar da ke Landan a ranar Talata.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Birtaniya ba ta bayar da amsa game da rahoton ba. Sai dai kuma, Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Gideon Saar ya ce matakin “Na da baƙanta rai”. Saar ya faɗa wa manema labarai cewa gwamnatin za ta yi zama na musamman a farkon mako mai zuwa don duba yadda za ta mayar da martani ga wannan mataki da “ba za a amince da shi ba”.
Birtaniya, kamar sauran ƙasashen Turai, na ta matsa lamba ga gwamnatin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ta kawo ƙarshen ƙawanya da toshe hanyoyin shiga Gaza, inda kwararru na ƙasa da ƙasa suka yi gargaɗin za a iya samun matsananciyar yunwa.
A watan da ya gabata Landan ta dakatar da tattaunawar janye haraji a kasuwanci da Isra’ila saboda yadda Isra’ilan ke ɗabbaka ‘manufofin danniya’ a Yammacin Kogin Jordan da Gaza, kuma ta aike da sammace ga jakadan ƙasar, kuma ta sanar da ƙarin takunkumai ga ‘yan kama-wuri-zauna a Yammacin Kogin Jordan.
Ministan Harkokin Waje David Lammy, wanda ya kira hare-haren baya bayan nan na Isra’ila da “mummunan sabon mataki a wannan rikicin”, a baya ma ya soki kalaman Smotrich kan kalaman yiwuwar korarwa da ruguza Gaza tare da mayar da mazaunan yankin zuwa wasu ƙasashe na daban.