TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya za ta fitar da jiragen yaƙi na KAAN 48 zuwa Indonesia
Shugaban Kasar Turkiyya ya taya murna ga Masana’antar Kayan Tsaro ta Turkiyya da Masana’antun Kera Sassan Jiragen Sama na Turkiyya, sakamakon nasarar kulla yarjejeniyar fitar da jiragen.
Turkiyya za ta fitar da jiragen yaƙi na KAAN 48 zuwa Indonesia
Turkiyya na habaka masana'antun tsaronta don dogaro ga kai a sha'anin tsaro. (AA) / AA
11 Yuni 2025

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da babbar nasara a masana’antun tsaron Turkiyya, inda ya ce za a fitar da jiragen yaƙi samfurin KAAN da ƙasar ta samar guda 48 zuwa Indonesia.

A wata sanarwa da ya fitar ta shafin X, Erdogan ya bayyana cigaba da “mai matukar muhimmanci kuma wanda aka yi maraba da shi” inda ya kuma ce za a samar da jiragen a Turkiyya kamar yadda aka sanya hannu kan yarjejeniya da Indonesia.

Yarjejeniyar ta kuma ƙunshi aiki da kokarin Indonesia na cikin gida wajen kera jiragen.

“Ina fata wannan yarjejeniya, wadda ta bayyana cigaba da kokarin da ake iya yi a yanzu a masana’antar tsaronmu, abu ne da zai amfanar da Turkiyya da Indonesia.” in ji Erdogan.

“Yarjejeniyar fitar da kayayyaki mai tarihi”

Ya kuma bayyana gamsuwa ga takwaransa na Indonesia, Shugaba Prabowo Subianto, inda ya bayyana muhimmiyar rawar da ya btaka don ganin an kulla yarjejeniyar.

Erdogan ya taya murna ga Masana’antar Kayan Tsaro ta Turkiyya da Masana’antun Kera Sassan Jiragen Sama na Turkiyya, tare da dukkan hukumomin da suke da hannu wajen tabbatar da yarjejeniya mai kafa tarihi.

Da yake jaddada aniyar gwamnatinsa wajen tallafa wa fannin, Erdogan ya ce “Za mu ci gaba da taimaka wa ba saurarawa ga dukkan kamfanonn samar da kayan tsaronmu don tabbatar da kara karfin masana’antar. Ina mika tsagwaron godiya ga ‘yan uwa maza da mata da ke aiki a wannan bangare.“

Jirgin yaki na KAAN, na ajin jiragen yai na zamani da ke da fasaha mafi kayau a yau, yana da injina biyu, wanda kowane ke da karfin tura kilogram 13,000, hakan ya ba shi damar samun sauri har zuwa matakn 1.8.

TAI na kuma duba nan gaba, tare da shirin samar da samfurin jirgin na zamani na shida da zai yi aiki da Kirkirarriyar Basira, tsarin maganisu na zamani, da iya aiki tare da jiragen yaki marasa matuki.

 

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us