NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Kebbi ta taya sarkin Gwandu murna bisa nasara a kan Jokolo a Kotun Koli
A ranar Laraba ne Kotun Ƙoli ta Nijeriya ta yanke hukucin korar ƙarar da sarkin Kebbi na 19 Alhaji Al-Mustapha Haruna Jokolo ya shigar yana kalubalantar sauke shi daga Sarautar Gwandu da gwamnatin jihar ta yi a 2005.
Gwamnatin Kebbi ta taya sarkin Gwandu murna bisa nasara a kan Jokolo a Kotun Koli
Gwamnatin Kebbi ta taya Sarkin Gwandu murna kan nasara da ya samu a Kotin Ƙoli
4 Yuni 2025

Gwamnatin jihar Kebbi ta taya Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar murnar nasarar da ya samu, sakamakon hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yi da ya tabbatar da nasararsa a shari’ar da aka yi da Sarkin Gwandu na 19 Alhaji Al-Mustapha Haruna Jokolo, abin da ya tabbatar da Alhaji Muhammadu Ilyasu a matsayin halastaccen sarkin Gwandu.

Wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al’ada na jihar Kebbi Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana nasarar a matsayin raba gardama kan shari’ar da aka shafe shekaru 20 ana yi a masarautar.

A ranar Laraba ne Kotun Koli ta Nijeriya ta yanke hukucin korar karar da sarkin Kebbi na 19 Alhaji Al-Mustapha Haruna Jokolo bai shigar yana ƙalubalantar sauke shi daga sarauta da gwamnatin jihar Kebbi ta yi a 2005.

An fara shari’ar ne dai tun daga matakin kotun jiha, har ta tuke zuwa Kotun Ƙoli.

Kwamishinan na watsa labarai na jihar Kebbi Alhaji Yakubu Ahmed ya ce gwamnati ta yi farin ciki da yadda hukuncin ya kawo karshen takkadamar, abin da ya yi mummunar illa ga kwanciyar hankali ga Masarautar ta Kebbi.

Sanarwar ta kuma yi kira ga Sarkin da ya yi nasara kan ya nuna dattako a nasarar da ya samu, sannan ya yi kokarin hada kan duka ahalin gidan saruta da suka yi takaddama, ta yadda za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’amuran sarautar gargajiya da ma masarutar.

Gwamnatin jihar Kebbi ta kuma jaddada goyon bayanta ga Sarkin na Gwanda, tare da fatan hukuncin zai bude sabon shafi na kwanciyar hankali da ci-gaba a masarautar da kuma jihar Kebbi baki daya

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us