NIJERIYA
2 minti karatu
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce sojoji sun kashe 'yan ta'adda 60 a garin Bita na Jihar Borno
Bayanai sun nuna cewa sojojin saman sun yi amfani da jiragen yaƙi ƙirar A-29 Super Tucano domin fatattakar ‘yan ta’addan.
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce sojoji sun kashe 'yan ta'adda 60 a garin Bita na Jihar Borno
Rundunar ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a safiyar ta Juma’a. / Nigerian army
30 Mayu 2025

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta kashe ‘yan ta’adda aƙalla 60 bayan farmakin da dakarun Rundunar Operation Hadin Kai suka kai ta sama da kuma ƙasa a maɓoyar ‘yan ta’addan a garin Bita da ke Jihar Borno da sanyin safiyar Juma’a.

Rundunar ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a safiyar ta Juma’a.

Duk da cewa ba ta yi ƙarin haske kan yadda harin ya gudana ba, amma mai sharhi da tattara bayanai kan al’amuran tsaro a Yammacin Afirka Zagazola Makama ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun ƙaddamar da harin ne da misalin ƙarfe 1:09 na dare kan sojojin 26 Task Force Brigade.

Ya bayyana cewa nan take dakarun suka samu taimako daga sojojin sama inda aka yi ta musayar wuta har zuwa 3:23 na dare.

Bayanai sun nuna cewa sojojin saman sun yi amfani da jiragen yaƙi ƙirar A-29 Super Tucano domin fatattakar ‘yan ta’addan.

A ‘yan kwanakin nan, hare-haren Boko Haram sun dawo a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya inda ko a kwanakin baya, sai da ‘yan ta’addan suka kashe sojoji da dama a harin da suka kai wani sansanin sojoji a ƙaramar hukumar Marte ta jihar Borno.

Haka kuma a ‘yan kwanakin nan ‘yan ta’addan sun kashe fararen hula da dama a yankunan jihar waɗanda suka haɗa da manoma da ‘yan kasuwa.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us