NIJERIYA
2 minti karatu
Julius Maada Bio: Shugaban Sierra Leone ya maye gurbin Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS
A jawabinsa na ƙarshe a matsayin shugaban ƙungiyar, Tinubu ya yi kira ga ƙasashen yammacin Afirka masu amfani da harshen Farasanci su koma cikin ƙungiyar ECOWAS.
Julius Maada Bio: Shugaban Sierra Leone ya maye gurbin Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS
Shugaba Tinubu ya jagoranci ƙungiyar na tsawon shekaru biyu / Reuters
23 Yuni 2025

An zaɓi Shugaban ƙasar Saliyo Julius Bio a matsayin shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

Bio ya maye gurbin Shugaba Bola Tinubu, wanda ya jagoranci ƙungiyar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban ƙasar Saliyo ya maye gurbin Tinubu ranar Lahadi yayin babban taron ƙungiyar na 67 da aka yi a birnin Abuja.

Kafin zaɓen, an yi ta hasashe cewa Shugaban ƙasar Senegal Bassirou Faye ne zai karɓi ragamar ƙungiyar.

Bio ya yi alƙawarin mayar da hankali wajen dawo da tafarkin dimokraɗiyya tare da ƙarfafa tafarkin yankin.

Ya kuma ambaci inganta haɗin kai ta fannin tsaro da haɗin ta fannin tattalin arziƙi da kuma samar da ma’aikatu da mutane za su yarda da su cikin ababen da zai mayar da hankali a kansu.

An zaɓi Tinubu a matsayin shugaban ƙungiyar ne a  karon farko a birnin Guinea-Bissau ranar 9 ga watan Juli ta shekarar 2023, kuma an sake zaɓensa bayan shekara ɗaya a birnin Abuja.

Shugabancinsa ya fuskanci ƙalubale wajen dawo da dimokraɗiyya  a yankin a lokacin Nijar da Mali da Burkina Faso sun fice daga ƙungiyar bayan an yi juyin mulki a ƙasashen uku.

Bio ya yaba wa Tinubu game da “ingantaccen shugabanci” da kuma “jajircewarsa wajen tattaunawa a yankin da farfaɗowar tattalin arziƙi da kuma samar da zaman lafiya”.

A jawabinsa na ƙarshe a matsayin shugaban ƙungiyar, Tinubu ya yi kira ga ƙasashen yammacin Afirka masu amfani da harshen Faransanci su koma cikin ƙungiyar ta ECOWAS.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us