Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a na Nijeriya, Lateef Fagbemi, ya ce Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (ICPC) sun ƙwato jimillar Naira biliyan 277 da dala miliyan 105m a shekarar 2024.
EFCC ta ƙwato naira biliyan 248 da dala miliyan 105, da kuma gidaje 753 a shekarar 2024, ita kuwa ICPC ta ƙwato tsabar kuɗi naira biliyan 29.685 da kuma kadarorin da darajarsu ta kai dala biliyan 966,900 na dukiyar da aka sace a shekarar.
Fagbemi, a wani taron bayyana kadarorin da aka ƙwato wanda aka yi a wannan makon a Abuja, ya ce Nijeriya ta yi nasarar dawo da wasu makudan kudade daga ƙetare, wanda hakan ya kara tabbatar da aniyar kasar ta fuskar bin diddigin yadda ake tafiyar da kuɗaɗe.
Ya kuma ce hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kara zage damtse wajen ƙwato kadarorin da ke da alaƙa da miyagun kwayoyi, tare da tabbatar da cewa haramtattun kudaden da aka samu ba za su ƙara rura wutar aikata laifuka ba.
"Game da dawo da kadaroriin da aka sace daga wasu kasashen da ke cikin tsarin Ma'aikatar Shari'a ta Tarayya, yana da mahimmanci a bayyana cewa daga 2017 zuwa yau, Ma'aikatar Shari'a ta Tarayya da ke aiki tare da hadin gwiwar takwarorinta da abokan hulda na kasa da kasa kamar a Amurka da Birtaniya da Ireland da Switzerland, an samu damar aiwatar da yarjejeniyoyi daban-daban, wanda ya kai ga dawo da kudaden tarar da aka samu da kuma dawo da kuɗaɗe har dala 763,734,000 da fama 6,472,610,” in ji shi.