20 Yuni 2025
An saka ranar buga wasan cin kofin garkuwar Charity Shield na Ingila, wanda za a yi tsakanin Liverpool da Crystal Palace.
Zakarar gasar Firimiya ta ingila a bana, Liverpool za ta kece raini da zakarar gasar kofin Emirates FA, Crystal Palace.
Za a buga wasan ne ranar 10 ga Agusta mai zuwa zai da tsakar ranar Lahadi da ƙarfe 3 na rana.
A babban filin wasan na Ingila, Wembley, za a buga wasan, kamar yadda aka saba.
A Birtaniya tashar TNT Sports za ta watsa wasan kai tsaye.