Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da gwamnatinsa sun zama "babbar matsala ga zaman lafiyar yanki," in ji Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, a ranar Asabar, yayin da hare-haren Isra'ila ke ƙara tayar da hankula a Gabas ta Tsakiya.
Erdogan ya jaddada cewa Isra'ila da gangan take lalata gine-ginen farar hula, ciki har da asibitoci, makarantu, masallatai, da coci-coci, tare da kai hari kan mata da yara marasa laifi.
"Bari na bayyana wannan a fili da gaskiya: da duk wannan zaluncin, tare da duk waɗannan hare-haren, gwamnatin Netanyahu ita ce babbar matsala ga zaman lafiya a yankin," in ji Erdogan yayin taro na 51 na Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC) a Istanbul.
Ya kuma bayyana cewa Falasɗinawan Gaza suna rayuwa cikin mawuyacin hali da ya fi muni fiye da na sansanonin ajiye fursunoni na sojojin Nazi na Jamus.
Erdogan ya kuma tuna da burin shugaban mulkin Nazi na Jamus, Hitler, wanda "ya jefa duniya cikin bala’i," yana mai cewa "burin Netanyahu na tsatsauran ra’ayin Yahudanci ba ya da wani amfani sai dai jefa duniya cikin bala'i."
‘Ta’addancin ƙasa’
Shugaba Erdogan ya kuma yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila na kwanan nan a Lebanon, Syria, Yemen da Iran, yana kiran hare-haren da aka kai a ranar 13 ga Yuni kan Tehran a matsayin "ta'addancin ƙasa."
Yayin da yake kare martanin Iran kan hare-haren Isra'ila, Erdogan ya bayyana cewa tashin hankalin Tel Aviv yana lalata ƙoƙarin diflomasiyya game da shirin nukiliyar Tehran.
"Yayin da take kara karfin nukiliyarta ba tare da bin ka'idoji ba — kuma wannan shi ne babban munafunci da Isra'ila ke nunawa — tare da hare-haren da aka kai a ranar 13 ga Yuni, gwamnatin Netanyahu ta yi niyyar lalata tsarin tattaunawa," in ji Erdogan.
Kai hari kan Iran yana nuna cewa "gwamnatin Netanyahu da masu aikata kisan gilla" ba su da niyyar warware matsalolin ta hanyar diflomasiyya, in ji shugaban.