Majalisar dokokin kasar ta samu bukatar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na neman amincewar ciyo bashin dala biliyan 21.5 daga waje da kuma lamuni na cikin gida naira biliyan 758 domin warware wasu basukan fansho.
Shugaban ya gabatar da bukatar ne da nufin samar da kudade don aiwatar da ayyuka masu mahimmanci a fannoni daban-daban na tattalin arziki - musamman kayayyakin more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da samar da ruwa - kamar yadda aka karanta a zauren majalisar dattawa yayin zamanta na yau.
An miƙa buƙatar ga kwamitin majalisar dattijai mai kula da basussukan cikin gida da waje don yin nazarin da ya dace, inda ake sa ran gabatar da rahoton nan da makonni biyu.
A wata bukata ta daban, Shugaba Tinubu ya kuma nemi amincewar Majalisar Dattawa don ba da takardun lamuni na Gwamnatin Tarayya a kasuwannin basussukan cikin gida don daidaita lamunin fansho a karkashin tsarin bayar da Gudunmawar Fansho.
Shirin bayar da lamunin ya kai naira biliyan 757.9.
Bukatar, da nufin samar da kudade masu mahimmanci a sassa daban-daban na tattalin arziki - musamman kayayyakin more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da samar da ruwa - an karanta a zauren majalisar dattawa yayin zaman majalisar na yau.
An mika shi ga kwamitin majalisar dattijai mai kula da basussukan cikin gida da waje don ci gaba da binciken majalisar, inda ake sa ran gabatar da rahoton nan da makonni biyu.
A wata bukata ta daban, Shugaba Tinubu ya kuma nemi amincewar Majalisar Dattawa don ba da takardun lamuni na Gwamnatin Tarayya a kasuwannin basussukan cikin gida don daidaita lamunin fensho a karkashin tsarin bayar da gudunmawar fansho.
Shirin bayar da lamuni ya kai naira biliyan ₦757.9.
A cewar wasikar Shugaban Ƙasar, bayar da lamunin na da nufin magance basussukan fansho da aka dade ana bin da kuma cika alkawarin gwamnati na ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya.
Bugu da ƙari, Shugaban Ƙasar ya bukaci amincewar majalisar dattijai don tara dala biliyan biyu daga kasuwannin cikin gida don tallafa wa saka hannun jari a sassan tattalin arziki masu mUhimmanci.
An kuma miƘa wannan bukata ga kwamitin kula da basussukan cikin gida da na waje domin tantancewa cikin makonni biyu.
Tun da farko dai, Shugaba Tinubu ya rubuta wa Majalisar Wakilai, inda ya nemi amincewar shirin karbo rancen waje na 2025-2026 da aka yi wa kwaskwarima.
A karkashin shirin, Shugaban ƙasar na neman rancen dala biliyan 21.5, da Yuro biliyan 2.2, da Yen biliyan 15 na Japan, da kuma bayar da tallafin Yuro biliyan 65.
A cewar wasikar, wacce shugaban majalisar ya karanta a zauren majalisar, an nemi lamunin ne da nufin magance tabarbarewar ababen more rayuwa a kasar da inganta ayyukan yi da dai sauransu.