Al’ummar ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun shiga cikin alhini bayan kisan killar da aka yi wa wasu mutum 38 da ‘yan bindiga suka sace suka kuma karɓi kuɗin fansar Naira miliyan 50.
Shugaban ƙaramar hukumar Kaura-Namoda, Mannir Haidara Kaura wanda ya tabbatar wa tashar talabijin ta Channels labarin, ya kuma ce mutum 56 ‘yan bindigar suka sace amma suka sako 18 daga baya.
Sannan mutum 18 din da aka sake, an kwantar da su a asibiti don kula da lafiyarsu sakamakon uƙubar da suka sha.
“Kuma tawagarmu da ta gwamnatin jiha na shirin zuwa wajen iyalan mamatan don jajanta musu,” in ji Mannir Kaura.
Channels TV ta ce wani mazaunin ƙauyen, Ibrahim Banga tun da fari ya sanar mata cewa tun wata ɗaya da ya gabata ne ‘yan bindigar suka kai hari garin tare da sace mutum 53.
Ya kuma bayyana yadda masu satar mutanen suka buƙaci a biya wa kowane mutum naira miliyan ɗaya, kuma sai da aka shafe lokaci kafin al’ummar garin su samu damar haɗa kuɗaɗen suka kai musu.
Banga ya ce sai dai abin takaici daga ƙarshe mutum 18 kawai aka sako.
Ya ce “Sai dai bayan dawowar su, sun ba da labarin yadda ‘yan bindigar suka yanka sauran mutum 35 ɗin, ɗaya bayan ɗaya.”
Nasarar sojoji a Jihar Neja
A wani labarin na daban kuma, dakarun rundunar sojin Nijeriya sun kawar da ‘yan ta’adda aƙalla 45 a ƙauyen Iburu da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja a ranar Juma’ar da ta gabata.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa bayan da aka samu wasu bayanan sirri da ke nuni da cewa ‘yan ta’adda a kan babura da dama na tunkarar Iburu da kauyukan da ke makwabtaka da shi, nan take hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta sanar da sojojin da ke cikin shirin ko ta kwana.
A cewar majiyoyin, an yi musayar wuta mai tsanani, inda sojoji suka kashe akalla ‘yan ta’adda 45.
Rahotanni sun ce mazauna kauyukan sun ƙirga gawarwakin mutane akalla 40 da ake kyautata zaton na ‘yan bindigar ne, tare da dimbin babura da aka lalata a yayin arangamar.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, wasu ’yan bindiga biyu da ke fafatawa tare da sojojin sun rasa rayukansu, yayin da wasu hudu ke karbar kulawar munanan raunukan harbin bindiga a wani asibitin gwamnati da ke babban birnin jihar.