TURKIYYA
4 minti karatu
Turkiyya na karɓar baƙuncin taron ministocin harkokin waje na ƙasashen OIC karo na 51
A lokacin da ake tsaka da yaƙi a Gaza da taɓarɓarewar rikicin Isra’ila da Iran, manyan jami’an diflomasiyya na OIC za su gana a Istanbul don bayyana matsaya guda da kare manufofin Musulmai a faɗin duniya.
Turkiyya na karɓar baƙuncin taron ministocin harkokin waje na ƙasashen OIC karo na 51
Turkish FM Hakan Fidan attends the OIC Extraordinary Council of Foreign Ministers Meeting in Jeddah, Saudi Arabia, 2025. / Photo: AA
20 Yuni 2025

Ministocin Harkokin Kasashen Waje na Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) za su gana a Istanbul a ranakun 21 da 22 ga Yuni a karo na 51, a yayin da rikici ke karuwa a Gaza, da Iran da ma Gabas ta Tasakiya baki ɗaya.

Taron zai mayar da hankali ne kan kalubalen siyasa, da zamantakewa da tattalin arziki da kuma al'adu da ke fuskantar kasashen Musulmai.

Fiye da wakilai 1,000, ciki har da jami'ai daga kasashe masu sa ido, da cibiyoyi masu alaƙa da OIC, da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ne ake sa ran za su halarci taron.

Ana sa ran Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai yi jawabin buɗe taron a ranar Asabar kan batun taɓarɓarewar yanayin tsaro a yankin.

A lokaci guda, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan zai karɓi ragamar shugabancin Kungiyar OIC daga hannun Lejeune Mbella Mbella na Kamaru tare da gabatar da jawabin buɗe taron.

A yayin taron na kwanaki biyu, ana sa ran ministocin za su tattauna batutuwan da suka shafi yaƙin da Isra'ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, da ƙoƙarin sake gina matsugunai a yankin da aka mamaye da kuma kira ga warware rikicin ta hanyar kafa ƙasashe biyu.

Taron zai kuma yi magana kan ɓacin yankin saboda hare-haren da Isra'ila ta kai kan Iran a baya-bayan nan, tare da yin nazari kan tasirinsu ga tsaron yankin da ma duniya baki ɗaya.

Haɗaka hadin gwiwa tsakanin ƙasashen OIC ta fuskar ƙalubalen da suke fuskanta na daga abubuwan da za a mayar da hankali a kai.

A cewar majiyoyin diflomasiyya, Fidan zai kuma bayyana aniyar Turkiyya ta ba wa muradun Falasdinawa fifiko a lokacin shugabancinsa. Zai sake nanata matsayin Ankara na tale-tale na a samar da kasashe biyu, wanda ke da muhimmanci ga samar da zmaan lafiya a yankin.

Ana kuma sa ran Fidan zai yi gargadi game da fadada ayyukan soji na Isra'ila - inda zia bayar da misalai ga hare-haren baya bayan nan da ta kai Lebanon, Syria da Yaman - sannan ya jaddada matakin Turkiyya na yin tir da wannan ta’addanci na Isra’ila.

Ana sa ran Iran za ta yi tir da ta'addancin Isra'ila

Ana sa ran ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi zai halarci zaman na ranar Asabar a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza faɗa tsakanin Isra'ila da Iran.

Majiyar ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce mai yiyuwa ne wani zama na musamman zai mayar da hankali kan hare-haren da Isra'ila ta kai a baya-bayan nan kan cibiyoyin nukiliya da na sojan Iran, ciki har da harin da aka kai tashar nukiliyar Khundab da ke birnin Arak.

Sojojin Isra'ila sun yi iƙirarin cewa sun kai hari kan wani injin sarrafa ruwa mai nauyi a wurin, wanda jami'an Yammacin Duniya ke zargin za a iya amfani da shi wajen ƙera plutonium mai aiki da makamai.

Turkiyya ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren, tare da bayyana su a matsayin keta dokokin ƙasa da ƙasa, tare da kare haƙƙin Iran na kare kanta da ƙasarta.

Pakistan za ta bayyana goyon bayanta ga Falasdinu

Mataimakin Firaministan Pakistan kuma Ministan Harkokin Wajen Ƙasar, Sanata Mohammad Ishaq Dar, ya sanar da cewa zai sake jaddada goyon bayan Islamabad ga al'ummar Falasɗinu tare da yin kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza.

Ana kuma sa ran Dar zai nuna buƙatar samar da kwanciyar hankali a yankin, da zaman lafiya da Indiya, da kuma taimakon jin ƙai na gaggawa ga Falasdinawa.

Malaysia za ta sake jaddada goyon baya ga hadin kan Musulmi

Ministan harkokin wajen Malaysia Dato' Seri Mohamad Hasan zai jagoranci tawagar kasarsa tare da gabatar da sanarwar kasa da ke bayyana matsayin Malaysia kan muhimman batutuwan da suka shafi hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar OIC.

Wadannan sun hada da goyon baya mara misaltuwa ga ‘yancin Falasdinawa na cin gashin kai, magance yawaitar kyamar Musulunci da kyamar addini, da habaka hadin gwiwar tattalin arziki, da nuna shirye-shiryen kasa da suka dace da manufofin kungiyar OIC.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us