Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) Ibrahim Kalin ya yi ganawa mai girma a ranar Talata tare da jami'an gwamnatin Iraki a Baghdad inda tattaunawar ta mayar da hankali kan kan tsaron kan iyaka da hadin gwiwar yaki da ta’addanci.
Da farko Kalin ya gana da Firaministan Iraki Mohammed Shi'a al-Sudani, sannan ya tattauna da shugaban kasar Abdul Latif Rashid.
Mataimakin Firaministan Iraki kuma ministan harkokin wajen kasar Fuad Hussein ma ya halarci taron, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana.
A wani bangare na ziyarar tasa, Kalin ya tattauna da ministan tsaron kasar Thabit Abbasi, da shugaban hukumar leken asiri Hamid al-Shatri, da jagoran kungiyar Kawancen ‘Yancin Kasa Khamis al-Khanjar, da kakakin majalisar dokoki Mahmoud al-Mashhadani.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna matakan hadin gwiwa don cim-ma "Turkiyya ba tare da ta'addanci ba" ta hanyar hada kai don tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasar da kawar da barazanar ta'addanci.
Bangaren Baghdad ya jaddada cikakken goyon bayansa ga Ankara a kowane mataki.
Tattaunawar ta kuma mayar da hankali kan damar da za ta bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, tare da yanayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
An dai tattauna batun zaman dar-dar tsakanin Iran da Isra'ila, inda bangarorin biyu suka yi nazari kan cigaban da aka samu a yarjejeniyar tsagaita wutar da ake aiki da ita.
Bayan haka, Kalin ya yi gana wa daban-daban da shugaban Turkmen na Iraki M. Seman Agaoglu da manyan jami'an ITC don duba yanayin tsaro a yankunan da Turkmen suke rayuwa, inda yake tsammani da fatan samun karin bayani kan shirye-shiryen zabe mai zuwa.